Kayatattun hotuna a wannan makon

Abubuwan da suka faro a wannan mako cikin hotuna

Kayatattun hotuna a wannan makon

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako cikin hotuna da Aminiya ta tattaro muku:

Shugaban Jamhuriyar Nijar na 11, Mohamed Bazoum ya karbi rantsuwar kama aiki da alkawarin magance matsalolin matalauciyar kasar. Karon farko da aka mika mulki tsakanin gwamnatocin farar hula a kasar Hoto: @mohamedbazoum.
Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ya sanar cewa Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin hada layukan waya da lambar dan kasa ta NIN. Hoto: @DrIsaPantami
Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, ta sanar cewa za ta ci gaba da yin rajistar masu zabe daga ranar 28 ga watan Yuni, 2021. Hoto: @inecnigeria.
Jami’an tsaro a Jihar Legas za su fara sanya kyamara a jikinsu yayin gudanar da aiki bayan Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da shirin. Hoto: @jidesanwoolu.
Sojin sama sun sa wa'adin gamawa da Boko Haram
Runduar Sojin Sama ta Najeriya na fargabar jirgin yakinta da ya yi batar dabo a yayin yaki da Boko Haram a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar, hatsari ya yi.
Ganin tafiyarsa London don ganin likita, Shugaba Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya su gano su kuma kamo ‘yan bindiga da masu taimaka musu. Hoto: @Buharisallau1.
Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da dauki matasa miliyan 50 aikin soji. Daga baya ya nemi afuwa cewa kalaman da ya yi a taron cikarsa shera 69, subul da baka ne.
Kasar Saudiyya ta sanar da tsare-tsaren sallolin Tarawih da Tahajjud na bana a masallacin Harami: Rage yawan raka’o’in sallolin, takaita Dawafi zuwa masu Umrah kadai, rufe famfunan Ruwan Zamzam, shiga Masallaci sai da izini, taikata wuraren yin Sallah da sauransu. Hoto: @hsharifain
Dakarun Gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun dakile yunkurin kifar da Gwamnatin Shugba Mahamadou Issoufou kwana biyu kafin rantsar da Shugaba Mohamed Bazoum. Sojojin da suka yi yunkin na tsare a halin yanzu. (Hoto: France24).
Bayan kwana shida ana fadi-tashi, an janye katafaren jirgin ruwa ‘Evergiven’ makare da kwantainoni ya makale a Mashigin Suez.
Babban attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote daga Najeriya da wasu gwamnonin Arewacin kasar sun halarci liyafar rantsar da Bazoum.