Kayyade ranakun cin kasuwa na jawo mana asara —’Yan tumatur

Masu sayar da kayan lambu a kasuwar tumatur ta Abuja da ke Deidei sun koka da yadda kayyade ranakun bude kasuwanni ke jawo masu asara. A farkon makon da ya gabata ne dai minisatan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello, ya kafa dokar da ta takaita lokutan cin kasuwa zuwa ranaku uku a mako […]

Kayyade ranakun cin kasuwa na jawo mana asara —’Yan tumatur

Tumaturin da aka kawo tun daren Asabar ba za a sayar ba sai ranar Litinin, inji ‘yan kasuwar

Masu sayar da kayan lambu a kasuwar tumatur ta Abuja da ke Deidei sun koka da yadda kayyade ranakun bude kasuwanni ke jawo masu asara.

A farkon makon da ya gabata ne dai minisatan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello, ya kafa dokar da ta takaita lokutan cin kasuwa zuwa ranaku uku a mako (Litinin, da Alhamis, da Asabar), a matsayin wani mataki na takaita zirga-zirgar jama’a don hana yaduwar annobar coronavirus.

Sai dai ’yan kasuwar sun ce hakan na sa kayan lambun nasu su lalace.

Shugaban ’yan kasuwar, Malam Adamu Umar Hudu, ya ce ‘yan sandan yankin ne suka tilasta masu bin umarnin, tun a farkon makon na jiya.

“Wadannan kwandunan tumatur da kake gani tun jiya Asabar suka iso kasuwar nan da dare, sai dai ba dama mu sayar da su yau Lahadi har sai zuwa gobe Litinin”, inji shi.

Shugaban kasuwar tumatur ta Abuja, Malam Adamu Umar Hudu

Shugaban ‘yan kasuwar ya ce matakin ya saba da bayanin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a farkon ayyana dokar takaita zirga-zirga a Yankin Babban Birnin Tarayya da kuma jihohin Legas da Ogun, inda ya ce dokar ba za ta shafi masu sayar da kayan abinci ko safararsa ba.

“A saboda haka muna kira ga mai girma ministan Abuja da ya duba lamarinmu, saboda yanayin kayan da muke sayarwa”, inji Malam Adamu.

Da karfe 11 na daren Litin 30 ga watan Maris ne dai Shugaba Buhari ya sanar da dakatar da ko wacce harka a Yankin na Babban Birnin Tarayya.