Kaza ta yi sanadin mutuwar mutum biyu

A makon jiya ne, wata kaza ta yi sanadin rasuwar mutum biyu masu suna Damina da Ali a kauyen Katogen Gargari da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa sannan mutum na uku ya jikkata. Wani makusancin mutanen mai suna Malam Bello ya shaida wa Aminiya cewa wata kazar gidan ce ta fada cikin rijiyar marar ruwa, […]

Kaza ta yi sanadin mutuwar mutum biyu
Kaza ta yi sanadin mutuwar mutum biyu

A makon jiya ne, wata kaza ta yi sanadin rasuwar mutum biyu masu suna Damina da Ali a kauyen Katogen Gargari da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa sannan mutum na uku ya jikkata.

Wani makusancin mutanen mai suna Malam Bello ya shaida wa Aminiya cewa wata kazar gidan ce ta fada cikin rijiyar marar ruwa, inda matar mai gidan ta gaya wa danta cewa kaza ta fada rijiya ga ’ya’yanta can suna kukan neman uwarsu.
Malam Bello ya ce bayan ta fada wa yaron ne sai ya ce zai je gona sai ya dawo zai ciro ta, amma da maigidan ya zo sai matar ta sake sanar masa cewa kaza ta fada a rijiya, inda har ya turo kekensa zai tafi gona sai ya jingine keken ya tube rigarsa ya shiga cikin rijiyar zai ciro kazar.
Ya ce bayan ya shiga ya dade ba a ji motsinsa ba ne sai matar ta sanar da mutanen unguwa cewa mijinta ya shiga rijiya amma ta ji shiru tun dadewa babu motsinsa, inda wani makwabcinsa da ya dawo daga kasuwa ya tarar da abin da ya faru ya tube ya shiga, amma shi ma sai aka ji shiru.
Malam Bello ya ce ana cikin wannan hali ne sai mutum na uku ya yi shiga rijiyar amma jm kadan ya fito ya fadi kasa saboda zafin da ya buge shi a ciki, inda nan take aka dauke shi cikin mawuyacin hali, sai aka kira wo jami’an kashe gobara suka ciro gawarwakin mutum biyu daga rijiyar.
Wakilinmu ya samu labarin cewa a lokacin da jami’an kashe gobara suka isa garin sai da suka yi feshin ruwa a cikin rijiyar, inda bayan dauko mutanen jami’in da ya shiga rijiyar ma ya jikkata saboda zafin da ke cikinta da rashin wadatacciyar iska.
Tuni aka yi jana’izar mutanen kuma jama’a daga makawabtan kauyen na ta zuwa Katogen Gargari don ta’aziyyar mamatan.