KCSF ta nemi a kafa hukumar kula da nakasassu a Kano
Ƙungiyar ta ce kafa irin wannan hukuma zai taimaka wajen kare haƙƙin nakasassu a jihar.
Ƙungiyar Kula da Al’umma Jihar Kano (KCSF), ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya kafa Hukumar Kula da Nakasassu domin kare haƙƙin mutane masu nakasa.
Da yake magana yayin taron manema labarai a ranar Laraba, Shugaban ƙungiyar, Mohammad Bello, ya jaddada muhimmancin kafa irin wannan hukuma domin tabbatar da shigar da mutane masu nakasa cikin harkokin rayuwar yau da kullum.
- Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Kano ta 2024
- ’Yan sanda sun kama mutum 721, sun ƙwato motoci 13 a 2024 a Borno
Ya ce hukumar za ta kula da aiwatar da dokokin da suka shafi nakasassu, tallafawa gwagwarmayar neman haƙƙinsu, da kuma ba su dama su bayyana matsalolinsu da buƙatunsu.
“Kafa Hukumar Kula da Nakasassu a Jihar Kano zai yi daidai da Dokar Nakasassu ta Najeriya ta 2019 da Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Hakkokin Mutane Masu Nakasa (UNCRPD).
“Wannan mataki zai bai wa mutane masu nakasa damar bayar da gudummawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa zaman lafiya a cikin al’umma,” in ji Bello.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta fifita kafa hukumar tare da ware isasshen kasafi don gudanar da ayyukan ta.
Har ila yau, ƙungiyar ta buƙaci a riƙa shigar da mutane masu nakasa cikin duk wani shiri da tsare-tsaren da suka shafi nakasassu.
Ƙungiyar ta yaba wa gwamnatin jihar bisa wasu matakan da ta ɗauka, kamar bai wa mutum sama da 5,000 kiwon lafiya kyauta.
Ta jaddada cewa akwai buƙatar ƙarin aiki don magance ƙalubalen da nakasassu ke fuskanta a Jihar Kano.