Kebbi na kashe Naira miliyan 280 duk wata wajen ciyar da dalibai
Kwamishinan Ilimi na jihar Kebbi Mohammad Magawata ya ce, gwamnatin Kebbi na kashe jumullar kudi na Naira miliyan 280 a duk wata a bangaren shirin ciyar da daliban makarantun gwamnatin jihar. Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan ne a yau Litinin a wajen horar da yadda ake aika tsabar kudi wanda asusun kula da kanan […]
Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu
Kwamishinan Ilimi na jihar Kebbi Mohammad Magawata ya ce, gwamnatin Kebbi na kashe jumullar kudi na Naira miliyan 280 a duk wata a bangaren shirin ciyar da daliban makarantun gwamnatin jihar.
Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan ne a yau Litinin a wajen horar da yadda ake aika tsabar kudi wanda asusun kula da kanan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta shirya, ya ce wannan shirin yana taimakawa ne, wajen rage adadin yaran da basu zuwa makaranta a kasar.
Mohammad Magawata, ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan 2 wajen samar tebura, kujeru da sauran abubuwan makaranta a wannan shekarar.