Kebbi ta kafa kwamitin binciken ma’aikatan bogi a kananan hukumominta
Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin Gwamna Atiku Bagudu ta kafa kwamitin tantance ma’aikatankananan hukumomi 21 da ke jihar a wani yunkuri na bankado ma’aikatan bogi a jihar.Kwamitin a karkashin jagorancin tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Alhaji Jelani Yawuri, ana sa ran ya samar da ingantanccen jadawalin ma’aikata da gano ma’iakatan bogi a kananan hukumomin.An dade […]
Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin Gwamna Atiku Bagudu ta kafa kwamitin tantance ma’aikatankananan hukumomi 21 da ke jihar a wani yunkuri na bankado ma’aikatan bogi a jihar.
Kwamitin a karkashin jagorancin tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Alhaji Jelani Yawuri, ana sa ran ya samar da ingantanccen jadawalin ma’aikata da gano ma’iakatan bogi a kananan hukumomin.
An dade ana zargin cewa ana tafka magudi, musamman ta hanyar kara yawan ma’aikata da tauye wa wasu ma’aikata hakkinsu, inda ake biyansu kasa da albashinsu.
Bayan sauke shugabannin kananan hukumomi da jami’an biyan kudi da sakatarorin kananan hukumomin da su ne ake zargi ana hada kai da su wurin almudahana ne gwamnatin ta kafa kwamitin da aka ba hakkin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi ta hanyar sai-na-ga-idonka.
Wakilinmu ya zagaya wasu kananan hukumomi domin ganin yadda binciken ke gudana, inda karamar Hukumar Kalgo, ya tarar da ma’aikata jingim suna jiran a tantance su, sabanin yadda suke fitowa a ranakun aiki.
A karamar Hukumar Bunza kuwa duk da wakilinmu ya iske ana aikin, shugaban kwamitin, Uwargida Esther Jatau ta ki yin magana da manema labarai, inda ta ce ba ta da hurumin yin haka.
A karamar Hukumar Dandi-Kamba, shugaban kwamitin Lauya Attahiru Maccido ya ce aikinsu na tafiya yadda ya kamata, kuma suna sa ran su kammala shi nan ba da dadewa ba.
Da wakilinmu ya tuntubi shugaban kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomi ta karamar hukumar kan zargin da ake yi cewa akwai ma’aikatan bogi da saninsu ne aka tantance su, sai ya ce bai san da su ba, kuma ya ce sun gamsu da yadda ake gudanar da aikin a karamar hukumar.
kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kebbi a wata takarda da ta ba manema labarai dauke da sa hannun shugabanta Kwamared Murtala Usman, ta koka kan rashin sanya ’ya’yan kungiyar a cikin aikin tantance ma’aikatan, inda ta yi kira ga duk ma’aikacin da ya ga an zalunce shi ya hanzarta kawo kokensa ga sakatariyar kungiyar domin a bi masa hakki, kungiyar ta kuma shawarci ma’aikata su bi doka da oda da kuma ba da hadin kai domin samun nasarar wannan aiki.