… Kebbi ta kasafta Naira biliyan 166
Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya gabatar da kasafin kudin bana na Naira biliyan 166 da miliyan 825 da dubu 48 da 92 ga Majalisar Dokokin Jihar. Gwamnan ya ce daga cikin kudin an ware Naira biliyan 39 da miliyan 939 da 502 da 373 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, […]
Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya gabatar da kasafin kudin bana na Naira biliyan 166 da miliyan 825 da dubu 48 da 92 ga Majalisar Dokokin Jihar. Gwamnan ya ce daga cikin kudin an ware Naira biliyan 39 da miliyan 939 da 502 da 373 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware Naira biliyan 126 da miliyan 885 da 719 don gudanar da manyan ayyuka. Gwamna Sa’idu dakingari ya ce an tsara kasafin kudin ne domin ya zama daidai da kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin kasashen duniya da kuma nan cikin gida. Gwamnan ya kuma ce kasafin zai bunkasa samar da ayyukan yi da abinci da kuma inganta yanayin rayuwar jama’a don ci gaban jihar.