Kebbi ta rasa mahajjaci na uku a Saudiyya
Mutum na uku a cikin maniyyatan Jihar Kebbi ya rasu kwanaki uku kafin fara aikin Hajji a kasar Saudiyya.
Mutum na uku a cikin maniyyatan Jihar Kebbi ya rasu kwanaki uku kafin fara aikin Hajji a kasar Saudiyya.
Hukumar kula da jin dadin alhazan jihar ta sanar cewa mahajjacin mai suna Alhaji Abubakar Abdullahi ya rasu ne a birnin Makkah sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban hukumar, Alhaji Farouk Aliyu-Enabo, ya sanar da cewa marigayi Alhaji Abubakar Abdullahi dan yankin Gulma ne daga Karamar Hukumar Argungu ta Jihar Kebbi.
Sanarwar ta kara da bayyana cewa an yi wa marigayin jana’iza a Masallacin Harami kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
- Jirgin sama ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi ya ɓace
- ’Yan bindiga sun hallaka sama da mutum 50 a Katsina
Ya kuma mika sakon ta’aziyyar hukumar da gwamnatin jihar ga iyalan mamatan tare da rika musu rahamar Allah.
A halin da ake ciki, hukumomin aikin Hajji sun shawarci maniyyata da su dauki matakan kariya musamman saboda yanayin tsananin zafin rana da ake ciki a Saudiyya a halin yanzu.
Hukumomin aikin Hajji na kasa da na jihohin Najeriya na ci gaba da gudanar da cibiyoyin kuka da lafiyar alhazansu a biranen Makkah da Madina.