Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma
Gwamnatin Kebbi ta yi shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin saukaka wahalar noma a jihar.
Gwamnatin Kebbi ta bullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin saukaka musu yin wahalar noma a jihar.
Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farrfado da aikin noma domin jihar ta cigaba da rike kambunta a bangaren noman shinkafa a Nijeriya.
Saboda haka ne ta gina karamin wurin noma na zamani a kananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta.
Wannnan a cewarsa, kari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin.
- Mayaƙan Boko Haram sun sace mata 319 a Borno
- EFCC ta kama motoci 21 maƙare da kayan abinci a hanyar fita ƙetare
Ya kara da cewa gwamnatin jiha ta biya kasonta na Naira miliyan 350 a cikin shirin RAAMP, wanda zai samar da hanyoyin mota masu tsawon kilo mita 240 domin manoma su samu saukin sufuri, gwamnati ta sanya miliyan 350 a shirin.
Shehu Mu’azu ya sanar da hakan a taron manema labarai na sati-sati da ma’aikatar yada labarai ta shirya.