Kek din wake
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan kuna lafiya da kuma cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin Kek din wake. Kayan hadi • Wake • Sukari • Bakin hoda • kwai • Bota Yadda ake yi:- Da farko uwargida za ki samu wake mai […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan kuna lafiya da kuma cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin Kek din wake.
Kayan hadi
• Wake
• Sukari
• Bakin hoda
• kwai
• Bota
Yadda ake yi:-
Da farko uwargida za ki samu wake mai kyau sai barza a inji. Idan aka kawo sai ki bakace domin duk bawo da bakin da ke jikin waken ya fita. idan kika tabbatar ya gyaru sosai sai ki bayar akai miki inji a nika shi ya yi laushi sosai. Sanann sai ki tankade. Sai ki ajiye a gefe daya. Sannan ki samo mazubin da za ki kwaba kek din a ciki sai ki zuba sukari da bota ki juya su sosai sanan ki kawo kwai ki fasa akai, ki ci gaba da juyawa. Idan kika tabbatar ya biyu. (anan wasu suna amfani da injin na mider wanda hanya ce da take da sauki da kuma kyau wajen kwabin kek) sannan sai ki dauko garin wakenki ki zuba tare da bakar hoda akan wancna kwabin sai ki ci gaba da juyawa kamar yadda ake yi wa fulawa. Idan kika gama sai ki dauko mazubin kek din ki shafa masa man bota a jiki sannan ki zuzzzuba kullun a ciki. Sannan sai ki jera su a abin da kike yin gashi da shi. Ki barshi na kimanin minti 20. Idan ya gasu za ki ji yana kanshi.