Keke da mota 1
Wani mai mota ne yana gudu za shi wani wuri sai kawai wani mai keke ya yi gilma masa, shi kuma ya buge shi. An tsaya ana cece-kuce, kawai mai keke ya ce a biya shi kekensa, mai mota ya ce shi ma haka. Da aka tafi kotu, alkali ya ji batun kowa sai ya […]
Wani mai mota ne yana gudu za shi wani wuri sai kawai wani mai keke ya yi gilma masa, shi kuma ya buge shi. An tsaya ana cece-kuce, kawai mai keke ya ce a biya shi kekensa, mai mota ya ce shi ma haka. Da aka tafi kotu, alkali ya ji batun kowa sai ya ce: “To ina mai keken da ya buge mai mota?” Mai keke ya tashi cikin mamaki ya ce: “Yallabai inji uban waye?” Alkali ya ce: “Ku kama shi ku kai jarun, ya zagi alkali.”
Daga Tukur Ruwaya Gargaje, Zariya 08064245780