Kelechi Nwakali ya sanya wa kulob din Arsenal hannu

dan kwallon Najeriya Kelechi Nwakali ya samu nasarar sanya wa kulob din Arsenal da ke Ingila hannu a kan Fam miliyan 2 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 800.Kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Sports Day ta kalato, an nuna dan kwallon ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara biyar.Ita ma Hukumar kwallon […]

Kelechi Nwakali ya sanya wa kulob din Arsenal hannu
Kelechi Nwakali ya sanya wa kulob din Arsenal hannu

dan kwallon Najeriya Kelechi Nwakali ya samu nasarar sanya wa kulob din Arsenal da ke Ingila hannu a kan Fam miliyan 2 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 800.
Kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Sports Day ta kalato, an nuna dan kwallon ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara biyar.
Ita ma Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta fitar da sanarwar cewa Kelechi Nwakali wanda ya taimaka wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) lashe kofin  duniya na matasa a bara, ya amince ya koma kulob din ne a kwanataragin shekara biyar.
Sanarwar ta ce hakan ya faru ne bayan kulob din ya gayyaci dan kwallon a watan Janairu da ya wuce don ya yi masa gwaji inda tuni ya amince da kwarewarsa da hakan ta sa suka kulla yarjejeniya.
Kamar yadda wani jami’i a hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ya sanar wanda bai so a ambaci sunansa ba ya ce “ba zan iya tantance ainihin kudin kwantaragin dan kwallon ba, amma ina da tabbacin kudin ba su gaza Fam miliyan biyu ba”.
A watan jiya ne dai aka ruwaito kocin Arsenal Arsene Wenger yana fadin kulob din ya kusa kulla yarjejeniya da ’yan kwallon Najeriya biyu Kelechi Nwakali da Samuel Chukwueze.  Yanzu za a iya cewa maganar kocin ta zama gaskiya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa