‘Kenwa a rijiya’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin summa amin. Kamar kullum, a yau na kawo muku labarin ‘Kuliya a rijiya’. Labarin ya yi nuni game da yadda idan za a gina ramin mugunta a gina shi kadan. A sha karatu lafiya.   Akwai wani yaro. Mahaifinsa […]

‘Kenwa a rijiya’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin summa amin. Kamar kullum, a yau na kawo muku labarin ‘Kuliya a rijiya’. Labarin ya yi nuni game da yadda idan za a gina ramin mugunta a gina shi kadan. A sha karatu lafiya.

 

Akwai wani yaro. Mahaifinsa manomi ne. mahaifin nasa kuma na fama da matsalar beraye dake addabarsa. berayen sun kasance suna ciye masa hatsinsa da kuma yi masa barna.

Rannan sai ya sayo wata Kenwa wadda ta yi nasarar cinye berayen gonan da kuma korar su.

A kullum sai yaron ya rika wulakanta wannan kenwar walau kama mata bindi ko kuma razanar da ita. Kawai yaron sai ya yanke shawarar jefa kenwar a rijiya.

Bayan ya wurga ta a rijiya, sai kenwar ta shiga ihun neman taimako wadda hakan ya sanya wani yaro ya zo ya ciro ta da kyar.

Sai Kenwar ta dau alwashin rama abin da yaron ya ma ta.

Bayan kwana biyu, sai kenwar ta gayyaci ‘yan’uwanta suka razana yaron. Garin gudu sai shi ma ya fada rijiya wadda da kyar aka fitar da shi.

Tare da fatan Manyan gobe za su kasance masu kirki da kuma tausayi.