Kenya ta fara yaki da shan barasa
A makon jiya ne kasar Kenya ta bayar da sanarwa a kan tsauraran matakan da ta dauka a kan shan barasa, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Mutane da dama na samun kulawa har ma an mayar da filin kallon kwallo cibiyar kula da masu matsalar shaye-shayen barasa.Wata mata mai suna, Anne Wanjiku […]
A makon jiya ne kasar Kenya ta bayar da sanarwa a kan tsauraran matakan da ta dauka a kan shan barasa, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Mutane da dama na samun kulawa har ma an mayar da filin kallon kwallo cibiyar kula da masu matsalar shaye-shayen barasa.
Wata mata mai suna, Anne Wanjiku ta kashe makudan kudi wajen sayan barasa har sai da ta kasa biyan kudin makarantar ’ya’yanta.
Anne Wanejiku wacce kowa a filin kwallon ke kira ‘cucu’ watau ma’ana ‘Kaka’ da yaren ‘yan kabilar Kikuyu, mai shekara 56, tana daya daga cikin mata biyar da ake kula da su saboda shaye-shayen barasar.
Tsauraran matakai na kwana-kwanan nan da gwamnatin kasar ta dauka ga masu shan barasa ba bisa ka’ida ba da kuma masu sha da basu kai shekarun doka ta kayyade ba, da kuma sabuwar cibiyar kula da masu matsalar shaye-shaye, na cikin sababbin tsarin dokokin kasar da aka fitar.
“Da idanuna na ga wadanda suka makance kuma suka rasa rayukansu sakamakon shan barasa,” inji ta. Daga nan sai ta nuna idonta guda cikin raha, tana mai cewa, “Na yi sa’a ni ido daya na rasa”. Kodayake, duk da haka ta ci gaba da shan barasa.
A cikin makonni uku da bude cibiyar kula da masu matsalar shaye-shayen barasa, an samu kafa tantuna a filin kwallon, inda mutanen da ke bukatar taimakon suka karu zuwa fiye da 700.
Duk wanda ya zo zai samu makwanci a cikin tantin, da abinci sau uku a rana da kuma kula da shawarwari, amma dole su zauna har watanni uku.
Hukumomin kasar suna kyautata zaton za a samu karin mutanen da za su kai dubu biyar kuma hakan ya sa suka fara kafa karin tantuna, amma akwai wani fili da aka kebe domin shakatawa, inda ake buga kwallo da kuma shan iska.
Wakilin BBC ya ce cikin mutanen da ya tarar akwai ‘yan sanda da lauyoyi har ma da wani likita, duk suna samun kulawa.
Wani mutum ya ce yana kewar gida, amma shi ba zai tafi ba sai ya kammala wa’adin zaman neman kulawar.
Mista Wa Iria, gwamnan garin ya ce matasan suna samun goyon baya daga kungiyar matasa da suka kafa, inda suke taimaka wa juna, suna kuma samun horo a kan aikin hannu da kananan sana’o’i.