Kenya ta harba tauraron dan Adam karon farko

Akalla kasashen Afirka 13 ne suka kera tauraron dan Adam 48.

Kenya ta harba tauraron dan Adam karon farko

Kasar Kenya ta harba tauraron dan Adam na farko, inda jirgin ’yan saman jannatin mai suna Taifa-1 ya tashi a cikin rokar Falcon 9 na SpaceX daga sansanin sojojin sama na Vandenberg a Kalifoniya.

Tauraron dan Adam din, wanda injiniyoyin kasar Kenya suka kera, ana sa ran zai samar da muhimman bayanai kan noma da samar da abinci da sauran fannonin da za su tallafa wa tattalin arzikin kasar.

Harba jirgin wani muhimmin ci gaba ne ga shirin sararin samaniyar Kenya, kuma ma’aikatar tsaron kasar da hukumar kula da sararin samaniyar Kenya sun bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar nasara ga al’ummar kasar.

An kera tauraron dan Adam din ne tare da hadin gwiwar wasu kwararru da ke kula da harkokin sararin samaniya a kasar Bulgeriya.

Kasar Kenya wadda ke da karfin tattalin arziki a Gabashin Afirka, na fama da fari mafi muni a cikin shekaru da dama bayan rashin samun ruwan sama tsawon shekara biyar a jere.

Don haka, ana sa ran shirin harba tauraron dan Adam din zai taimaka wajen samar da bayanai kan yadda za a tallafa wa shirye-shiryen samar da abinci a kasar.

Nasarar da aka samu wani bangare ne na wani gagarumin yunkuri da kasashen Afirka ke yi na kirkire-kirkiren kimiyya da bunkasa shirye-shiryen sararin samaniya.

Zuwa shekarar 2022, akalla kasashen Afirka 13 ne suka kera tauraron dan Adam 48, sai dai babu wanda aka kaddamar daga nahiyar, sai a wasu kasashen Turai, a cewar Space in Africa.

Masar ce kasa ta farko a Afirka da ta aika da tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya a 1998, kuma a cikin 2018, Kenya ta harba nata na farko na gwaji daga tashar sararin samaniya ta kasa da kasa.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50