Kenya ta kama jigon al-Shabbab da ke kashe ’yan jarida
’Yan sandan kasar Kenya sun kama wani jigo a kungiyar al-Shabbab ta kasar Somaliya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa gidan sashin Ingilishi na rediyon BBC Landan.’Yan sandan sun hakikance cerwa wanda iaka kamar shi ne wani tsohon dan jarida mai suna Hassan Hanafi, da ake zargi da kashe ’yan jarida a kasar Somaliya […]
’Yan sandan kasar Kenya sun kama wani jigo a kungiyar al-Shabbab ta kasar Somaliya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa gidan sashin Ingilishi na rediyon BBC Landan.
’Yan sandan sun hakikance cerwa wanda iaka kamar shi ne wani tsohon dan jarida mai suna Hassan Hanafi, da ake zargi da kashe ’yan jarida a kasar Somaliya kamar yadda wasu majiyoyi suka ce.
Sai dai mutumin da aka kama din ya musanta cewa shi ne Hassan Hanafi lokacin da ake yi masa tambayoyi, inji majiyar.
Al-Shabab ta kai hare-hare masu yawa a Somaliya da Kenya, inda a watan Satumban da ya gabata mayakan kungiyar suka kashe mutum 67 a harin da suka kai rukunin shagunan Westgate da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Majiyoyin tsaro a Somaliya sun ce an kama Hanafi ’yan kwanakin da suka gabata a Nairobi sakamakon hadin kan hukumomin leken asiri na kasashen biyu kamar yadda wakilin BBC a Nairobi Abdullahi Abdi ya ruwaito.
An ce Hanafi ya je Kenya ne domin jinya lokacin da ’yan sanda suka kama shi a kamen da ba a cika yi ba a tsakanin kasashen waje ba domin kama ’yan al-Shabbab.
Sai dai mutum – da har yanzu ke amsa tambayoyin masu yaki da ta’addanci na Kenya – ya nace cewa ba shi ne Hanafi don haka a sake shi.
An ce Hanafi ya shiga banagren soja na al-Shabab ne a shekarun bayan nan, bayan ya yi fice a aikin labarai da gidan rediyon Andalus, kafar labarai ta al-Shabbab a Somaliya.
’Yan jarida a Somaliya sun dade suna zarginsa da kashe abokan aikinsu, inji wakilin BBC. Kimanin ’yan jarida 20 ne aka kashe a kasar Somaliya a cikin shekara uku da suka gabata.