Keshi ya aika wa Emenike sakon ta’aziyya

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya aika wa dan kwallon gaba a kungiyar, Emmanuel Emenike sakon ta’aziyya na rashin mahaifinsa da ya yi. Emenike wanda ya buga kwallonsa a kulob din Fernabahce na Turkiyya ba ya cikin ’yan kwallon da Keshi ya gayyato wadanda za su fafata a gasar neman […]

Keshi ya aika wa Emenike sakon ta’aziyya
Keshi ya aika wa Emenike sakon ta’aziyya

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya aika wa dan kwallon gaba a kungiyar, Emmanuel Emenike sakon ta’aziyya na rashin mahaifinsa da ya yi.

Emenike wanda ya buga kwallonsa a kulob din Fernabahce na Turkiyya ba ya cikin ’yan kwallon da Keshi ya gayyato wadanda za su fafata a gasar neman gurbi a gasar cin kofin Afirka (Nations Cup kualifier) da Najeriya za ta yi da Chadi a wannan wata da muke ciki. Ma’ana ba ya cikin ’yan kwallon da Stephen Keshi ya gayyato don su fafata a wasan saboda rashin da aka yi masa.
Emenike yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da ake ji da su a halin yanzu tun bayan ya samu nasarar shiga kungiyar a shekarar 2011.
dan kwallon ya buga wa kungiyar Super Eagles wasanni 35 kawo yanzu.
Mahaifinsa ya rasu ne a karshen makon jiya bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram