Keshi ya nemi NFF ta biya shi diyyar fiye da Naira biliyan 1

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya shigar da kara inda yake neman Hukumar kwallon kafa NFF ta biya shi diyyar Naira biliyan daya da miliyan 200 a bisa korar da ta yi masa ba bisa ka’ida ba. Idan za a tuna, hukumar NFF ta kori Koci Stephen Keshi ne daga […]

Keshi ya nemi NFF ta biya shi diyyar fiye da Naira biliyan 1
Keshi ya nemi NFF ta biya shi diyyar fiye da Naira biliyan 1

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya shigar da kara inda yake neman Hukumar kwallon kafa NFF ta biya shi diyyar Naira biliyan daya da miliyan 200 a bisa korar da ta yi masa ba bisa ka’ida ba.

Idan za a tuna, hukumar NFF ta kori Koci Stephen Keshi ne daga kan mukaminsa a watan jiya bayan ta same shi da laifin neman aikin horarwa a Kwaddebuwa alhali a lokacin yana da kwantaragi da Najeriya. Dokar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA da ta Afirka (CAF) sun hana wani koci ya nemi yin aiki da wata kasa alhalin yana horar da wata kasa ba tare da ya ajiye mukaminsa ba. A kan haka ne hukumar ta kafa kwamitin bincike inda ta samu Keshi da laifi sannan daga baya ne ta bayar da sanarwar korarsa. Daga nan ne hukumar ta maye gurbin Keshi da Sunday Oliseh kuma tuni sabon kocin ya fara aiki.
Keshi dai ya bayyana bukatar biyansa wannan kudi ne ta hannun Lauyansa da ke garin Kaduna a wata kara da ya shigar kotu.
Sai dai rahotannin da ke fitowa daga Hukumar NFF ta nuna Shugaban Hukumar Mista Amaju Pinnick ya ce karar da Keshi ya shigar ba ta da wani tasiri da za ta yi a kan hukumar, don ba ta da tushe balle makama. Ya ce duk da yake Keshi yana da damar ya shigar da kara amma kararsa ba za ta yi tasiri a kan hukumar ba, tun da an kore shi ne a bisa ka’ida.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja