Keshi ya sake zama Kocin Eagles a karo na uku

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sake daukar Stephen Keshi a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles a karo na uku. An yi bikin sanya hannu a kwantaragin ne a tsakanin Keshi da NFF a sakatariyar Hukumar da ke Abuja.Yarjejeniyar ta nuna […]

Keshi ya sake zama Kocin Eagles a karo na uku

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sake daukar Stephen Keshi a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles a karo na uku.

An yi bikin sanya hannu a kwantaragin ne a tsakanin Keshi da NFF a sakatariyar Hukumar da ke Abuja.
Yarjejeniyar ta nuna Keshi zai jagoranci ragamar kungiyar ne a tsawon shekara biyu. Sai dai Hukumar ta gindaya masa wadansu sharudodi da suka hada da kawar da nuna wariya wajen zabo ’yan kwallo da kuma sanar da hukumar wajen daukar wani mataki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Haka kuma hukumar ta gindaya wa kocin sharadin ya rika tuntubarta kafin ya zartar da duk wani hukunci da kuma alkawarin yin aiki da jami’an hukumar ba tare raini ko nuna gaba da kyama ba.
Stephen Keshi dai shi ya taimaka wa Najeriya lashe kofin Afirka a shekarar 2013 amma kuma ya kasa tabuka abin a-zo-a-gani a bara, a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil da kuma kasa hayewa da Najeriya gasar cin kofin Afirka a bana.
Bayan sun raba gari da Hukumar NFF jim kadan an kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, sai Hukumar ta dauke shi a matsayin na wucin-gadi inda ta rika biyansa a kan kowane wasa.
Daga baya hukumar ta dakatar da shi inda kungiyar ta zauna a karkashin kulawar mataimakinsa Daniel Amokachi kafin yanzu da ta sake daukarsa a matsayin kocin kungiyar a karo na uku.
Keshi ya amince da duk sharudodin da aka gindaya masa a kwantaragin kuma sha alwashin yin aiki tukuru don farfado da martabar kungiyar, inda ya nemi hadin kan magoya baya da daukacin ’yan kasa wajen ganin sun mara masa baya don ya samu nasara.
Sai dai tuni wasu suke guna-gunin yadda Hukumar ta sake ba Keshi dama a karo na uku alhali akwai kwararrun kococin da za su iya tabuka abin a-zo-a-gani idan an ba su dama.