Keshi zai sanya hannu a sabon kwantaragi a watan gobe -NFF
A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana cewa kocin Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ana sa ran zai sanya hannu a sabon kwantaragin cigaba da horar da kungiyar Super Eagles kafin Najeriya ta yi wasa da Sudan na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka da […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana cewa kocin Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ana sa ran zai sanya hannu a sabon kwantaragin cigaba da horar da kungiyar Super Eagles kafin Najeriya ta yi wasa da Sudan na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka da zai gudana a kasar Maroko a shekara mai zuwa, kamar yadda kafar sadarwa ta Premium Times ta kalato. Najeriya dai za ta yi wasa da Sudan ne a watan gobe watau na Oktoba a filin wasa na Ondurman da ke kasar.
Rahoton ya ce an ji Sakatare-Janar na Hukumar NFF, Barista Musa Amadu yana bayanin cewa idan kocin ya sanya hannu a kwantaragin zai kawo karshen dambarwar da ke tsakaninsa da Hukumar tun bayan da aka gama gasar cin kofin duniya a Brazil a watan Yulin da ya gabata.
A wasanni biyu na neman zuwa gasar cin kofin Afirka da Najeriya ta yi da kasashen Kongo da Afirka ta Kudu ta samu maki daya ne kacal da hakan ya sa wadansu suka tika hasashen an samu wannan koma-baya ne saboda matsalar rashin sabunta kwantaragin kocin don bai san matsayinsa game da cigaba ko rashin haka na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ba.
Idan za a tuna, kocin ya sanya hannu ne a wasanni biyu da Najeriya za ta yi watau a tsakanin Kongo da Afirka ta Kudu da hakan ta sa yanzu kwantaragin wucin gadi ya kare a tsakaninsa da NFF.