Keyamo ya soke jinginar da filayen jiragen saman da gwamnatin Buhari ta yi
Ya kuma dakatar da shirin kafa kamfanin jrage na Nigeria Air
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya soke jinginar da filayen jiragen saman da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi.
Ya kuma dakatar da ci gaba da aikin kafa kamfanin jiragen sama mallakin Najeriya na Nigeria Air,har sai abin da hali ya yi.
- Cin Zarafin Shehunnai: Mai Dubun Isa ya janye kalamansa
- Sojojin Nijar sun bukaci a fitar da jakadan Faransa ta karfin tsiya
Aminiya ta rawaito yadda gwamnatin da ta gabata ta cefanar da filayen jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Malam Aminu Kano da ke Kano.
To sai dai lokacin da yake zagaya filin jirgin saman Legas a ranar Alhamis, Festus Keyamo, a ziyararsa ta farko tun bayan zama Minista, ya ce an dakatar da cefanar da filayen da kuma shirin fara Nigeria Air har sai nan gaba.
Ayyukan guda biyu dai sun matukar janyo ce-ce-ku-ce saboda an aiwatar da su ne ’yan kwanaki kafin cikar wa’adin Buhari.
Ya kuma ce kamfanin CAAC na Amurka, wanda ya kunshi kungiyar filayen jiragen sama ta Amurka da kamfanin Mota Engil Africa da Mota Engil Nigeria ne suka samu damar jinginar flayen.