Khadija Bukar Abba ta fara haduwa da fushin mazabarta
’Yar Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tarmuwa da Damaturu da Gujba da Gulani a Jihar Yobe, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ta hadu da fushin jama’ar mazabarta yayin ganawa da magoya bayanta a garin Damaturu don sharar fagen neman sake tsayar da ita a zabe mai zuwa. Wasu daga cikin magoya bayanta sun fasa […]
’Yar Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tarmuwa da Damaturu da Gujba da Gulani a Jihar Yobe, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ta hadu da fushin jama’ar mazabarta yayin ganawa da magoya bayanta a garin Damaturu don sharar fagen neman sake tsayar da ita a zabe mai zuwa.
Wasu daga cikin magoya bayanta sun fasa kurjin da ke damunsu wajen nuna mata cewa, me ya kawo ta tunda a baya ta gaza zuwa don ta yi musu jaje da ta’azziyar rashe-rashe da barnar dukiyoyin da suka yi fama da su don haka suka ce ba su yi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yar majalisar ta gana da magoya bayanta a Damaturu inda wasu daga cikinsu suka fara tanka mata cewa, me ya hana ta zuwa a baya lokacin da mafi yawa daga cikin yankunan da take wakilta ke fama da tashe-tashen hankulan ’yan kungiyar Boko Haram da suka haddasa rasa rayukan jama’a da barnar dukiyoyi?
Malam Bulama daga karamar Hukumar Gujba ya shaida wa Aminiya yadda ’yar majalisar ta yi watsi da su na tsawon lokaci musamman halin da suka shiga na rashin kwanciyar hankali inda har yanzu wasu na gudin hijira amma ta gaza zuwa domin yi musu jaje ko ta’aziyyar rashe-rashen da suka yi fama da su balle ta kai musu tallafi.
Wani matashi dan Jam’iyyar APC kuma mai goyon bayan ’yar majalisar da ya bukaci a sakaye sunansa cewa ya yi Hajiya Khadija ba ta nuna musu halacci ba, domin kuwa a cewarsa babu irin halin da ba su shiga na yadda za su yi ta ci zaben da ya gabata ba, amma a karshe ta yi watsi da su.
Ya ce dama sun dana bakarsu saboda sun san za ta sake nemansu kuma ga shi hakan ta taso, don haka a yanzu sun san ciwon jikinsu ba Khadija kadai ba, duk wani dan siyasa a shirye suke su yi waje rod da duk wani dan takara da bai cika alkawari ga al’umma.
Ya ce tunda ta je majalisa babu abin da ta yi musu na ayyukan raya kasa balle su matasa da suka mara mata baya ta kula da su.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don samun daya daga cikin jami’an ’yar majalisar ko ita kanta don jin ta bakinsu kan lamarin ya ci tura.