Khadijah Abdullahi Iya: Gyaran al’umma ta hanyar tatsuniya

Khadija Abdullahi Iya marbuciya ce, malama ce, mai fafutuka, kuma uwa

Khadijah Abdullahi Iya: Gyaran al’umma ta hanyar tatsuniya

Khadijah Abdullahi Iya ta shekara 14 tana fafutuka

Allah Ya yi wa Khadijah Abdullahi Iya baiwar iya bayar da labari; amma ba a bayar da labarin kawai ta tsaya ba, don kuwa tana dabbaka wannan baiwa wajen amfani da tatsuniyoyi don sauya al’umma.

Saboda cimma wannan manufa kuma har wata kafa ta kirkiro wadda take alkinta al’adu da kyawawan dabi’unmu na Afirka ta hanyar mayar da tatsuniyoyinmu zanannun hotuna masu motsi, wato animation ko cartoon a Turance.

Wani abin sha’awa game da Tauraruwar tamu ta yau shi ne, tana wannan ne domin cimma burinta na inganta al’umma — ta yi amanna cewa sai yaran Afirka sun fahimci tatsuniyoyinsu da al’adun da suka gada kaka da kakanni sannan za su san inda suka dosa.

Ita dai Khadijah Abdullahi Iya lauya ce, ’yar kasuwa, marubuciya, mawallafiya, sannan mai fafutukar sauya rayuwar al’umma.

Ita kwararriya ce wajen yaki da cin zarafin mutane saboda bambancin jinsi, har ma tana da takardar shaidar kwarewa a wannan bangaren.

Sannan kuma kwararriya ce mai takardar shaida a harkar gudanarwa (Certified Management Consultant, CMC) kuma mamba a Kungiyar Kwararru a Harkar Gudanarwa (Fellow Institute of Management Consultants, FIMC).

Fafutukar shekara 14

Ta yi digirinta na farko (a Jami’ar Abuja) a Nazarin Shari’a (Law) da na biyu (a Jami’ar Jos) a Shari’a da Diflomasiyya.

Hajiya Khadijah ta assasa hidimomi da dama na sauya rayuwar al’umma da kasuwanci.

A yanzu haka ita ce Shugabar S.I. Magazine Limited, ita ta assasa Beyond Mentors Inc., kuma take jagorantar Tatsuniya Network — wani matashin kamfani mai mayar da tatsuniyoyi da tarihin Najeriya zuwa sigar zanannen hoto mai motsi (animation).

Ita ce Shugabar kungiyar Al’ummar Mata a Afirka (Women Community in Africa), ga ta kuma ta shafe fiye da shekara 14 tana aikin jinkai da taimakon al’umma.

Tauraruwar tamu ta samu kyaututtuka da lambobin yabo da dama, wadanda suka hada da kautar bunkasa ilimi mai inganci a Najeriya daga Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula Masu Fafutukar Inganta Ilimi (CSACEFA).

Tasiri a rayuwar al’umma

A shekarar 2020 Tarayyar Kungiyoyi Masu Fafutukar Kare Hakkokin Bil-Adama da Mata ta Duniya suka karbi sunanta a cikin wadanda za a bai wa Kyautar Zaman Lafiya a bangaren Fasahar Yaki da Tashintashina da kuma, a 2021 a bangaren Samar da Al’umma mai Dorewa.

Hajiya Khadijah tana da ’ya’ya da jikoki, sannan burinta na ganin rayuwar al’umma ta inganta bai tsaya a fatar baka ba. Burinta a rayuwa shi ne ta gadar da wani abu da zai yi tasiri a rayuwar al’umma.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos