Khadijah Ibrahim: Darussan da na koya a rayuwa

Khadijah Ibrahim ita ce matar Jakadan Chadi a Najeriya. Ta yi aiki da Majalisar dinkin Duniya a Chadi, daga bisani ta yi aikin kwalliyar gida a New York, Amurka. Ta bayyana wa Zinariya bambanci tsakanin matan Najeriya da kuma Chadi Tarihin RayuwataSunana Khadijah Ibrahim, ni matar Jakadan Chadi a Najeriya ce. An haife ni a […]

Khadijah Ibrahim: Darussan da na koya a rayuwa
Khadijah Ibrahim: Darussan da na koya a rayuwa

Khadijah Ibrahim ita ce matar Jakadan Chadi a Najeriya. Ta yi aiki da Majalisar dinkin Duniya a Chadi, daga bisani ta yi aikin kwalliyar gida a New York, Amurka. Ta bayyana wa Zinariya bambanci tsakanin matan Najeriya da kuma Chadi

Tarihin Rayuwata
Sunana Khadijah Ibrahim, ni matar Jakadan Chadi a Najeriya ce. An haife ni a yankin Kudancin Chadi, yankin da mafiya yawan jama’arsa Kiristoci ne. Mijina daga Arewacin Chadi yake. Muna da ’ya’ya bakwai wadanda suke karatu a kasashen waje.
Sunan mahaifina Alhaji Dudu, mu biyu ne a wurinsa, daga ni sai kanina. A yanzu ni marainiya ce gaba da baya, saboda Allah Ya yi wa mahaifana rasuwa. Na yi karatuna a Faransa inda na karanta Huldar Jakadanci. Daga nan na fara aiki da Majalisar dinkin Duniya, inda na zama mai jagorantar Hukumar UNDP a Chadi. Bayan mijina ya zama wakilin Chadi a Majalisar dinkin Duniya da ke New York, sai muka koma can. Hakan ya sanya na daina aiki da Hukumar UNDP.
Bayan wadansu shekaru ne sai na fara koyon aikin zayyanar cikin gida a wata makaranta mai suna School of Decoration a New York. Daga baya mijina ya dawo Chadi, amma haka na tsaya a can saboda ’ya’yanmu da ke karatu a lokacin. Bayan sun kammala sai muka dawo Chadi.
Abin da ya faru da ni ina karama
A lokacin da muke kanana mun yi abubuwa da dama. Yanzu shekarata 62, abubuwa sun canza sosai. Ina iya tuna rayuwar makaranta a lokacin, nakan tuna irin rayuwar da ni da abokaina muka yi, inda muke yin komai tare. A lokacin ina makarantar kwana ce, makarantar Kiristoci ce da ake kira ‘Secreca’, tana daya da cikin makarantu mafiya inganci a Chadi a lokacin. Daga nan aka fara yaki, komai ya daidaice. Za ka samu idan kana Arewa to ka rasa wani abokinka daga Kudu. A lokacin an raba Ndajamena babban birnin kasar biyu, a nan komai ya kasance a bai-bai.
Dangantaka da iyayena
A al’adarmu dole ka rika kiran mahaifiyarka da sunanta na gaskiya. A lokacin da nake kauye ina kiran mahaifiyata da sunanta. Bayan mun koma birni sai na samu yara suna kiran mahaifiyarsu da ‘mama’, hakan ya sanya na rika jin wani iri a lokacin da nake kiran mahaifiyata mama. Abin mamakin shi ne, ba ta ji komai ba, domin ta fahimci canjin wurin zama ne ya kawo hakan. Wata rana kakata ta wurin uwa ta kawo mana ziyara, sai ta ji na kira mahaifiyata da mama, hakan ya girgiza ta matuka, ba ta san lokacin da ta mike a fusace, sannan ta lakada mini duka ba, ba na taba manta wannan lokacin. Daga nan na rika kiran mahaifiyata da asalin sunanta har ta bar duniya.
Al’adarmu
Abin kunya ne a al’adarmu da na farko ya rika kiran mahaifiyarsa da mama, amma sauran ’ya’ya za su rika kiran mahaifiyarsu da mama.
Yadda nake kallon Najeriya
Najeriya babbar kasa ce da tafi yawan jama’a a Afirka. Abuja kamar wadansu garuruwan kasashen Turai take, ba kamar sauran garuruwan kasashen Afirka ba. A nan mutane aikin da ke gabansu suke yi, ba su da lokacin ziyarar ’yan uwa da abokai. Ina son yanayin kasar nan.
Ina son ’yan Najeriya saboda suna da gaskiya, kuma ba masu son fada ba ne. Chadi da Najeriya suna da abubuwa iri daya da yawa. Idan ina Najeriya nakan ji kamar a Chadi nake. Abin da yake matukar burge ni shi ne, yadda mutanen Najeriya suke matukar girmama na gaba da su. Wannan al’ada ce mai kyawu, ba a samun hakan a wadansu kasashe.
Farin cikin zama uwa
Na yi matukar farin ciki bayan na yi haihuwar farko. A al’adarmu akwai abubuwan da ba su kamata wacce ta yi haihuwar farko ta rika yi ba. Misali akwai abubuwan ba a barin wacce ta yi hahihuwar farko ta rika yi. Misali daukar jariri a kowane lokaci. Za a lura maka da jaririn, inda a lokacin za ka ga yadda ake lura da shi, kana koya, idan ka ci gaba da haihuwa sai ka ci gaba da lura da jariranka. Ina farin ciki domin na ga dukkan ’ya’yana sun girma. Babban farin ciki ne ma yanzu da na zama kaka, kasancewar ina da jikoki uku, dukkansu mata ne.

kewar dangi
Nakan yi kewar ’yan uwana kowane lokaci, sai dai da ina tare da su ba zan yi wadansu ayyukan ba. Ni uwa ce don haka ya kamata na kasance mai lura da iyalina.
kungiyoyi
A yanzu haka muna da kungiyar matan jakadun kasashen duniya mai suna ASOHOM, inda muke taimakon mata wajen lura da ’ya’ya.
Yadda na shiga kungiyar ASOHOM
An kafa kungiyar ASOHOM ne tun a 1993, don haka bayan na zo Najeriya sai na shiga kungiyar. Matar Jakadan Japan a Najeriya Le Mai Anh Shoji ce shugabar kungiyar a Najeriya, tana kuma kokari wajen tafiyar da kungiyar. Mukan yi zama kowace Alhamis din mako na biyu na kowane wata.
Burin kungiyarmu
Mu inganta rayuwar marayu. A yanzu muna ziyartar gidajen marayu da suke Abuja, inda muke ba su kyaututtuka, mu kuma taimaka musu don rayuwarsu ta inganta.
Bambanci tsakanin matan Najeriya da Chadi
Matan Najeriya na matukar kokari, suna aiki, sannan suna gwagwarmaya da maza wajen neman mukamai, haka ga bangaren wadanda ba sa aikin gwamnati ma za ka gan su a kan hanya suna yin abin da zai samar musu taro da sisi. A Chadi da zarar mace ta yi aure, sai ta daina karatu. Amma a Najeriya za ka ga mata mai ’ya’ya hudu, amma tana karatu. Wannan abin burgewa ne.
Mutane abin koyi
Nelson Mandela shi ne babban mutumin da nake koyi da shi, zan kuma ci gaba da koyi da shi har abada. Mutum ne na kwarai, mai kwazo da kuma kwatanta gaskiya.
kasashen da na ziyarta
Ina yawaita ziyartar Afirka ta Kudu saboda yadda nake son Mandela. Na je Nimibia da Tanzania da Amurka da sauransu.
Farin cikina
Ina jin farin ciki duk lokacin da na taimaka wa wani.
Nasarori
Haihuwar ’ya’ya babbar nasara ce a wurina. Ba ya ga haka na zama kaka, sannan na auri miji nagari da yake matukar sona.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da shi a makaranta. Daga nan muka shaku sosai. Daga baya ya je karatu Italiya, inda ya kammala a 1975, daga nan muka yi aure.
Tufafin Najeriya da na fi so
Ina so shadda. Ina son tufafin Yarabawa musamman idan suka sanya leshi, suka daura zane, sannan suka daura gwaggwaro.
Abincin Najeriya da na fi so
Ina son alale musamman ma idan an yi shi da kifi ko nama, sannan idan aka yi shi da man ja. Na fara cin sa a Maiduguri ne.
Darussan da na koya a rayuwa
Na koyi darasin in rika hakuri, sannan in yarda da kaddara mai kyawu ko akasin hakan. Ko yaushe nakan ce Alhamdulillahi.
Abubuwan da nake so a tuna ni da shi
Ban yi abubuwa da dama ba a rayuwa, amma ina so mutane su rika tunawa da ni a matsayin wacce ta taimaki al’umma.