Duk wanda ya cinye kuɗin goron Sallan malamai ya gaggauta dawo da su —Gwamnan Sakkwato

Duk wanda ya san ya rike kudin nan ya mayar da su nan take,” in ji gwamnan

Duk wanda ya cinye kuɗin goron Sallan malamai ya gaggauta dawo da su —Gwamnan Sakkwato

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya gargadi jagororin hukumar malamai na ƙananan hukumomi da suka yi ruf da ciki kan kuɗin goron Sallah da gwamnatin jihar ta bayar su gaggauta dawo da kudaden.

Gwamnan ya jaddada idan masu hannu a sama da faɗi da kuɗin goron Sallan suka ki dawo da su za su haɗu da ɓacin ransa.

Gwamna ya yi gargadin ne a lokacin da yake magana da magoya bayansa a gidan gwamnatin jihar.

Ya nuna ɓacin ransa kan halayyar wasu jami’an kuɗi a ƙananan hukumomi da suka hana wa ma’aikata dubu 30 da gwamantin jiha ta amince a ba su.

“Duk wanda ya san ya rike kudin nan ya mayar da su nan take, ko a dauki mataki mai tsauri kansa.

“Duk mai tunanin zai saci kudin gwamnati ya ci banza kuma to ya sauya tunani,” a cewarsa.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa