Khashoggi: Shugaba Trump ya goyi bayan Saudiyya a daidai lokacin da wasu ’yan gidan sarautar ke shirin yin bore

A daidai lokacin da wasu ke tofin Allah tsine a kan kisan dan jarida Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiyya na da hannu a kai, wasu daga cikin ’yan gidan sarautar sun fara shirye-shiryen yin bore tare da hana Yarima Mohammed bin Salman zama sarki nan gaba kamar yadda Reuters ta ruwaito daga wata majiya […]

Khashoggi: Shugaba Trump ya goyi bayan Saudiyya a daidai lokacin da wasu ’yan gidan sarautar ke shirin yin bore

Khashoggi Shugaba Trump

A daidai lokacin da wasu ke tofin Allah tsine a kan kisan dan jarida Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiyya na da hannu a kai, wasu daga cikin ’yan gidan sarautar sun fara shirye-shiryen yin bore tare da hana Yarima Mohammed bin Salman zama sarki nan gaba kamar yadda Reuters ta ruwaito daga wata majiya daga masarautar.

Da yawa daga cikin yarimomin masarautar da ’yan uwa na gidan sarautar Al Saud suna bukatar samar da canjin magajin sarautar, amma suna tsoron bayyana borensu a fili saboda Sarki Salman, mahaifin yariman mai shekara 82 yana raye, domin suna tsammani sarkin ba zai amince a canja sunan dansa ba, kamar yadda jaridar ta jiyo.

Don haka, sai suka fara shirin tattara iyalan gidan ta yadda idan Allah Ya dauki ran sarki Salman, Yarima Ahmed bin Abdulaziz mai shekara 76 wanda kani ne a wajen sarkin Salman kuma baffan yarima na yanzu zai maye gurbinsa.

Sai dai duk kokarin da jaridar ta yi na jin ta bakin yarima Ahmed ko wakilinsa ya ci tura.

Shi dai Yarima Ahmed shi kadai ne kanin da suke uwa daya uba daya da sarki Salman, kuma majiyar ta bayyana cewa zai samu goyon bayan iyalan gidan da jami’an tsaro da wasu kasashen ketare.

A watan Oktoba ne yarima Ahmed ya dawo birnin Riyad bayan ya yi kimanin wata biyu da rabi a kasashen waje. A lokacin da ba ya kasar, an jiyo shi yana sukar masarautar a lokacin da yake yi wa masu zanga-zanga jawabi a birnin Landan inda suke tofin Allah tsine da addu’ar durkushewar mulkin gidan Al Saud.

Ahmed yana daya daga cikin masu zaben sarki 3 cikin 34 da suka ki amincewa da nada Mohammad bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado a shekarar 2017.

Masarautar Saudiyya na da daruruwan yarimomi, kuma ba kamar sauran masarautu na Turai ba inda akwai wanda dole shi ne mai jiran gado wato babban dan sarki. A Saudiyya, tsarin shi ne da sarki da wakilan gidajen sarautan ne za su zauna su zabi mai jiran gado da suka ga ya cancanta.

Wani babban jami’in kasar Amurka ya bayyana cewa sun nuna wa Saudiyya cewa za su goyi bayan yarima Ahmed wanda ya taba rike Mataimakin Ministan Harkokin Cikin Gida na kusan shekara 40 ya zama mai jiran gado, kamar yadda majiyar ta kara.

 …Muna tare da Saudiyya- Shugaba Trump

A wani bangaren kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya samu labarin sautin muryar Jamal da aka dauka a lokacin da ake kashe shi, amma kuma bai bukatar ya saurara.

A cewarsa, “sautin muryar na wahala ne. ba dadin ji,” kamar yadda Trump ya shaida wa jaridar Fod kamar yadda AFP ta ruwaito.

Sai dai kuma kamar yadda wasu suka bukata, Shugaba Trump ya ce ba zai zargi yarima bin Salman ba duk da cewa rahoton Hukumar Leken Asiri wato CIA ya nuna cewa akwai hannun yariman a kisar dan jarida Khashoggi.

Da aka tambayi Trump a kan ko bin Salma ya masa karya ne lokacin da suka zanta a game da kisar, sai ya ce, “ban sani ba. Amma dai abin da na sani shi ne mutane da yawa sun ce bai da masaniya.

“Ya fada min cewa bai da masaniya a kai. Ya fada min wannan maganar kusan sau biyar a lokuta daban a cikin kwanaki da ba su wuce biyar ba.”

Sai dai Trump ya bayyana cewa watakila wasu mutane na kusa da Yariman suna da hannu, amma sai ya tabbatar da cewa shi fa yana tare da Saudiyya domin abokiyarsu ce. “Ni fa ina tare ne da abokiyarmu, wadda ta kasance muna ma’amala mai kyau a bangarori da dama.”