Ki gyara gidanki

Tsafta tana da matukar mahimmancin a rayuwar ‘ya mace. Ko ya kike, matar aure ce ke, budurwa, ko bazawara dole ki kasance kina da tsafta saboda babu wanda yake son kazamar mace. Ayau za mu yi bayani ne a kan tsaftar muhalli wato na gida. Mata da dama ba su cika kula da tsaftar muhallinsu […]

Ki gyara gidanki
Ki gyara gidanki

Tsafta tana da matukar mahimmancin a rayuwar ‘ya mace. Ko ya kike, matar aure ce ke, budurwa, ko bazawara dole ki kasance kina da tsafta saboda babu wanda yake son kazamar mace. Ayau za mu yi bayani ne a kan tsaftar muhalli wato na gida.

Mata da dama ba su cika kula da tsaftar muhallinsu ba, sai ka ga mace fes ta dau wanka ta sa kaya masu kyau ta yi kwalliya abun sha’awa amma in ka ga gidanta, falonta, ko daki ko ban-daki ko kicin, abun ba a cewa komai. Wannan ba hali ba ne mai kyau, shi gida yana da bukatar gyara. Ko yaya gidanki yake, duk rashin kyawunsa ke za ki gyara abin ki ya yi kyau. Ko da a gidan kasa kike, in kika kasance mai share gidanki da gyara shi gaba daya, ba za ki taba jin kunya ba ko da kuwa a ce gwamnan garinku zai kawo muku ziyara.

 

GYARAN FALO:

Ki kasance kullum kina share falonki safe da yamma idan baki da yara masu bata wa. Ko kuma yanayin yadda yake datti misali idan kina da yara, ki rika nade shimfidar daki  (carpet) kina jan kujeru kina share karkashinsu ko da sau 2 zuwa 3 ne a sati. Idan kin share sai ki yi goge (mopping) idan kina da tiles a falon kenan. Bayan haka sai ki goge talabijin da tebur da ake dora talabijin din.  Mata a nan suna gazawa sosai.

 

GYARAN dAKI:

Kullun idan kika tashi da safe ki gyara dakinki. Ki gyara gado, ki yi shara. Ki goge kan madubinki, ki sa turaren wuta. Ki kasance kina daga karkashin gado kina sharewa ko da sau daya ne a wata saboda ba ki san lokacin da datti ke shiga ba. Idan kina haka, za ki huta da  kyankyasai da kwari har da su bera da sauransu.

 

GYARAN BAN-dAKI:

Ki rika wanke ban-daki ki a kullum. Ya kasance yana daya daga cikin ayyukanki na sassafe. Wanke ban-daki na da matukar amfani, saboda za ki kare kanki daga cuttutuka kala-kala. Zai hana kudaje, kwari da kyankyasai zama a ban-dakin ki. Ki rika amfani da hypo ko bleach wajen wanke ban-daki irin na zamani (in akwai hali).  Idan kuma na tsugunnawa ne kamar shadda to ki rika amfani da izal kina wanke ban-dakin da shi. Sauran kayan wanke ban-daki ma ki nema kamar su dettol, happic, klin, da sauransu. Idan kika dage kina wanke ban-dakinki kullum to ke kanki zai ba ki sha’awar amfani bare idan kin yi baki ba za ki ji kunya ba.

 

GYRAN KICIN:

Kicin (dakin dafa abinci) na daya daga cikin wajen da ya kamata a ce kina kula da su saboda waje ne na dafa abinci. Idan ba shi da tsafta, abincin da za a dafa ma ba zai yi tsafta ba. To kin ga dole ki kasance mai tsaftace kicin idan har kina so ki samar da abinci mai inganci. Babu wacce take so ta yi girki a ga kuda a ciki ko wani kwaro, saboda babu wanda kuwa zai iya cin abincin.

 

Kafin ma ace kin dora tukunya, yi kokari ki gyara kitchen din tukunna. Ki share, ki goge duk inda ya kamata. Kaman kan gas cooker idan kina dashi, ko ki share wajen murhu idan da ita ce kike amfani. Ke kanki za ki fi jin dadin girkin idan kika kimtsa wajen. Da an gama cin abinci kuwa ki tattare kwanukan ki wanke su, saboda tara wanke wanke shi ke janyo kuda da sauran kwari kuma yana sa warin kicin.

 

GYARAN WURIN AJIYE ABINCI (STORE):

Store shi ne wajen da ake ajiye kayan abinci, kamar  shinkafa, masara, wake, gero, da sauransu. Ki rika fitar da kayan kina share wurin da ake ajiyarsu akalla sau 1 zuwa 2 a wata.  Don idan ba haka ba kwari da bera za su iya fasa buhu su yi barna ba ki sani ba ko su bata kayan abincin saboda haka ’yar uwa sai ki rika kula.

 

TSAKAR GIDA:

Idan kina da tsakar gida kuma akwai bishiya to a kullum ki rika sharewa ko ki sa a share. Idan kuma ba ki da bishiya amma akwai tsakar gidan, to shi ma a kullum yakamata ki share saboda ba za a rasa datti ba.

 

LABULE DA KAFET: 

Ba kowace mace ba ce ta damu da wanke labulai da kafet dinta ba.  Sai ki ga wata a shekara sau daya kacal take wankewa, wannan ba karamar kazanta ba ce. Koda ba sa nuna datti ’yar uwa je ki kade labulanki ki gani idan ba ki ga tulun kura ta taso ba. Wannan kurar za ta iya sa mura. Don haka ya kamata ki rika wanke labulan ki akalla sau 3 ko 4 a shekara.

Kafet (Carpet) kuma wasu matan in ba kala suka ga ya canza ba, ba za s uyi tunanin a wanke ba. Haka za ki ji da zarni da wari da tsami amma duk a haka ake zama ake kwanciya da cin abinci. ’Yar uwa yakamata ki rika bayar da wankin kafet dinki akalla sau biyu a wata musamman idan kina da yara.

 

CIRE YANA:

Wannan ma mata da yawa ba sa kula da cire shi. Ya kamata ki rika kula da gidanki, a duk lokacin da kika ga yana a daki, falo, ban-daki, kicin, wurin ajiye kayan abinci, tsakar gida koma ina ne to ki cire. A ido ma ba shi da dadin gani, kuma shi ma akwai kura a tattare da shi wanda kan iya janyo mura. Hausawa na cewa yana kan janyo talauci amma dai ban san inda suka samo wannan bayani ba.

 

TURAREN GIDA:

Bayan duk kin gama gyara gidanki kada ki manta da abu daya mai mahimmanci,  wato kamshi. Za ki iya amfani da turaren wuta na gida ko room freshners ko diffusers a gidanki domin samar da kamshi mai dadi.

Daga karshe ina fata ’yar uwa za ki dage wajen tsaftace muhallinki.

 Zainab Umar Baffa

Ita ce ta kirkiro da Cibiyar Tallafa wa Al’umma  (MAB) kuma tana zaune ne tare da iyalinta a garin Abuja.