Kibiyar tsautsayi 1
Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar 2 ga watan Janairu Ba sai an gaya maka ba, yanayin zaman zugum din da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Alhaji Bala da matarsa Ladidi, tare da ’yarsu Zuwaira wadda ke gefe daya tamkar ruwa ya ci ta: “Zama hakan fa ba zai kawo wani sauyi […]
Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar 2 ga watan Janairu
Ba sai an gaya maka ba, yanayin zaman zugum din da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Alhaji Bala da matarsa Ladidi, tare da ’yarsu Zuwaira wadda ke gefe daya tamkar ruwa ya ci ta: “Zama hakan fa ba zai kawo wani sauyi daga wannan tsautsayi da ya same mu ba, ta yaya za a ce yarinyar nan na da juna biyu kuma har ya kai watanni biyu ba tare da mun sani ba?’’ Ladidi ce ta fadi hakan a lokacin da Alhaji Bala ya kura mata idanuwa cike da son ya dora alhakin wannan sakacin a kanta.
Abin da Alhaji Bala bai sani ba shi ne, duk yadda yake mamakin ‘yarsu Zuwaira ta aikata wannan abin kunyar, matarsa Ladidi ta fi shi yin wannan mamakin. Sai dai ita ta yi imani da maganar da ke cewa, “BABU kARFI A CIKIN YI WA ALLAH BIYAYYA, KUMA BABU DABARA A CIKIN BARIN SAbAWA ALLAH FACE DA TAIMAKON ALLAH.’’ Ta yi imani da hakan ne tun daga ranar auren wata kawarta wadda suka shaku matukar shakuwa mai suna Lubabatu.
Lubabatu ta kasance yarinya mai hankali da tunani, mai ilimin addini da na zamani tare da girmama na gaba da ita. Zan iya cewa lalle ta karba suna’ya mace kuma tauraruwa a cikin ‘yan mata, musamman halin kamun kai da kowa ke yi mata shaidarsa. Sai dai a ranar aurenta, ta tsinci kanta a cikin wani halin kunci da damuwa sanadiyar azal din da ta fada kanta! Domin kuwa kwanaki kamar goma kafin ranar, wani saurayi mai suna Sadau ya yi awon gaba da budurcinta, wanda ta kasance tana karewa da rayuwarta tsawon shekaru goma sha uku.
Sadau da Lubabatu sukan hadu ne a makarantar da suke karatu tare, inda suke tattauna matsalolin da suka addabi al’umma na lalacewar tarbiya. Sai dai duk da cewar dukkansu mutanen kirki ne, sun dauki kansu masu cikakken tsarki. Sun manta da cewar hatta wannan haduwar tasu ta saba wa shari’a.
Sai suka take laifinsu suka mayar da laifin wasu abin kallo da zargi. Wanda hakan ne ya janyo Kibiyar tsautsayi ta illata su.
Wata rana da dare, Sadau ya je gidansu Lubabatu domin yi mata murnar aurenta da ake shirin yi, sai aka yi rashin sa’a, shaukin rabuwa da juna ya debe su, kafin ka ce sisi, Shaidan ya kada musu gangar musiba ba su ankara ba sai ga shi sun aikata abin da ba su shirya aikatawa ba. Domin kun san sharrin shaidan ya wuce wasa.
Shigowar Ladidi dakin da Lubabatu ke zaune, shi ne ya yi sanadiyar katsewar dogon tunani da nazarin da ta kebe kanta tana yi a daidai lokacin da sauran jama’a ke wurin sheke ayar buki. “Ladidi mene ne hukuncin macen da aka daura wa aure alhali wani namiji ya sadu da ita da kwanaki kadan kafin aurenta?’’ Lubabatu ce ta tambaye ta, ba kuma tare da ta tsaya jin amsarta ba, ta ci gaba da cewa “Ladidi tabbas na fahimci cewa jarrabawa tana fadawa kan kowa, kuma babu wanda yake iya tsira daga sharrin shaidan sai wanda Allah Ya kare. Kafin in sanar da ke abin da ya faru da ni, ina son ki amsa min wannan tambayar; Mene ne hukuncin wadda wani namiji ya sadu da ita lokaci kadan kafin aurenta, kuma mene ne hukuncin auren da aka daura mata a cikin wannan hali?’’