Kicibus da dan kishin kasa na gaske
Hatta zubin simintin farfajiyar gidan duk sun sha ado da launukan fari da kore.
Da wani maraice mai cike da gajimare, ranar Alhamis 8 ga Satumban 2022, yayin da nake tafiya kan titunan garin Biu, a Karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno, na yi kicibis da wannan gidan da aka kawata da fenti na musamman kuma mai jan hankali.
Komai na gidan ya sha ado da fentin launin kore-fari-kore, wato dai launukan tutar Najeriya.
- Najeriya @62: Jawabin Buhari ga ’yan Najeriya a takaice
- Nigeria@62: Yadda matsalolin tsaron Najeriya za su iya zama tarihi – Masana
Da rufin gidan da tankin ruwan da aka dora a sama da katungun ginin da kyauren gidan, kai hatta zubin simintin farfajiyar gidan duk sun sha ado da wadannan launukan.
Akwai abin ban sha’awa sosai ga wanda ya gani. Hakan ne ya sa na ga dacewar in san ko wane ne wannan mutumin kwarai da kishin kasarsa ya shallake gaban tunanin mutum.
Don haka sai na nemi jin shin gidan wane mutum ne wannan daga bakin direbanmu kuma dan jagoranmu, Malam Salisu, wanda yake aiki a Jami’ar Rundunar Sojin Kasa ta Biu (NAUB), wanda ya san kan dawan garin na Biu.
A cewarsa, gidan wani mutum ne mai matukar kishin kasa, wanda saboda tsananin kishin da yake yi wa kasarsa, ake masa lakabi da “Mista Najeriya” aka kuma fi saninsa da sunan “Green, White, Green”.
Na ce da Malam Salisu ya tsaya a gaban gidan domin in samu damar kure masa kallo, wala Allah ma in samu damar arba da wannan mutumin arzikin.
Ina tare ne da Alhaji Sultan Hassan wanda yake aminin arziki. Shi ma cewa ya yi ba za a bar shi a baya ba ba tare da bata lokaci ba sai muka tsunduma neman Mista Najeriya, ko kuma “Mista Green, White, Green, kamar dai yadda aka fi sanin sa.
Mun kwankwasa kyauren gidan. Ba a dade ba sai wata daddadar murya ta amsa sallamarmu, wani ne mai suna Samson, wanda ashe dan Mista Najeriya ne.
Bayan gaisuwa irin ta al’ada tare da gabatar da kanmu, sai muka zayyana masu manufarmu, cewa ginin gidan nasu ya kayatar da mu kuma muna son ganin mahaifinsa.
Ya fada mana cewa akwai bukatar gaggawa a Babban Asibitin Biu, inda can ne mahaifin nasa yake aiki, wadda ta sa lallai ne ya garzaya asibitin.
Duk da haka sai da muka yi tattaunawa mai tsayi da shi dan, inda muka kara jaddada masa niyyarmu ta mu sadu da wannan gagarumin dan Najeriya; kawai sai muka rankaya zuwa asibitin Alhamdu lillah, ya samu damar gabatar da aikin sannan aka sanar da shi cewa muna nan dakonsa a gidansa.
Ya fice daga wajen aikin domin ya koma gida ke nan nan sai muka yi sabani.
Da muka fahimci hakan, ba mu yi wata-wata ba wajen komewa zuwa wannan kyakkyawan gidan nan nasa. Mun tarar da Samson da ya tarbe mu ya fada mana cewa mahaifin nasa yana daga ciki.
Shigar mu gidan ke nan sai Dokta Dibal Arhyel Wandali, Mista Najeriya ko Mista Green White Green, cikin shiga ta musamman, wacce aka kawata da launukan kore da fari ya tarbe mu da kyakkyawar musafaha, inda ya yi mana lale maraba da zuwa kayataccen muhallinsan nan da ya sha ado da korayen launuka.
Ba tare da bata lokaci ba ya yi mana iso zuwa kuryar turakarsa, wacce ya yi wa matukar kawatawa.
Shakka babu, komai a cikin turakar ya sha ado ne da launin kore da fari, tun daga rufinsa har zuwa daben simintinsa.
Katangun turakar da kayan alatu da adon cikinsa har ma da kujerun ciki, duk sun sha fenti da ado irin na launin tutar Najeriya.
Mai dakinsa ita ma ta yi mana kyakkyawar tarba. Bayan ta gaishe mu, ta yi mana tayin lemun kwalba da ruwa.
Mun shafe lokaci muna tattaunawa da Dokta Wandali tare da iyalinsa, tamkar dai mun shaku da juna na tsawon lokaci.
Sai kuwa aka yi katarin cewa Alhaji Sultan Hassan ya san wani babban Jami’in soja da ya yi ritaya. Eya Kwamanda John Dibal, wanda bai dade da shigowa garin ba shi ma, ya garzaya zuwa gidan.
Shin wane ne wannan dan kishin kasan da har launukan kasarmu suka yi naso a zuciyarsa, ta yadda har wani zai ji yana burge shi tare da jin kishi da shi a kan haka?
Dokta Wandali kwararren mai gwaje-gwaje ne a dakin gwaji na asibiti, wanda ya kuma goge a fagen kafawa tare da kula da dakunan gwaje-gwajen, sannan yana aiki a Babban Asibitin Biu da ke Jihar Borno.
Ya fara aiki ne a wannan matakin tun 1987, sannan yana da alfahari da kasancewarsa dan Najeriya. Wadannan ba boyayyun abubuwa ba ne ga duk wadanda suka san shi.
Galibi yakan sanya tufa mai launin kore da fari da kuma koren sannan yana bikin tunawa da ranar ‘yancin Najeriya tare da abokai da iyalai da makwabta da kuma yara kanana, inda yake musu ‘yan kyaututtuka.
Dukkanin motocinsa, su ma ya yi masu fentin kore da fari kore.
An haife shi ranar 19 ga Oktoban 1963, a garin Wandali, garin da a yanzu yake a yankin Karamar Hukumar Kwaya Kusar ta Jihar Borno.
Ya yi karatun firamare a firamaren Wandali daga 1971-1977. Daga nan ya wuce zuwa Kwalejin Gwamnati ta Maiduguri, inda ya kammala a 1982.
Jim kadan bayan nan, ya tsinci kansa cikin mutum 60 ’yan asalin Jihar Borno da suka samu guraben karatu a Cibiyar Koyar da Kiwon Lafiya mai suna Polish Medical Institute (L.P. Pavlov) da ke a kasar Bulgaria. Ya kammala karatun a 1986.
Sannan ya samu kansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABUTH) daga 1991 zuwa 1992.
Ya yi Hidimar Kasa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Askarawan da ke Gadin Fadar Shugaban Kasa a Barikin Sani Abacha, da a yanzu ake kira da Mogadishu Military Cantonment Hospital, Abuja, daga 1992 zuwa 1993.
Dokta Wandali ya kuma yi aiki a Kwalejin Tarayya kan Lafiyar Dabbobi da Gwaje-gwajen Fasaha (FCVMLT), da Cibiyar Nazarin Lafiyar Dabbobi ta Kasa da ke Vom a Jihar Filato daga 1998 zuwa 1999.
Sannnan ya yi aiki a Jami’ar Jos daga 2003 zuwa 2005, inda a 2018 ya sake komewa jami’ar domin karo karatu.
Ya kuma yi aiki a matsayin dan agaji na sa-kai a kasar Rwanda na tsawon shekara biyu-daga 2007 zuwa 2009.
Ya kasance mai duba jarrabawa daga waje, na daliban da ke karatun aikin gwaje-gwaje a dakunan bincike na fiye da shekara 15 yanzu.
Bugu da kari yana daga cikin wadanda suke tsare-tsaren inganta harkokin kiwon lafiya a Najeriya.
Mutum ne mai magana da yaruka da dama, inda bayan harshensa na uwa (Bura), ya iya Hausa da Turancin Ingilishi, sannan gogagge ne a harshen Bulgarisky (yaren Kasar Bulgaria) da kuma harshen Kirwanda (harshen mutanen Rwanda).
Magidanci kuma yana da ’ya’ya. Yana da shaukin daga sunan Najeriya, inda yake damawa a harkokin da suka jibanci kiwon lafiya sannan yana kallon shirye shirye na musamman na talebijin domin shan iska.
A halin da muke żaune a turakarsa, sai Alhaji Sultan Hassan ya kira wani abokinsa a waya, yana tambayarsa cewa shin ya san Mista Najeriya da jarabarsa ta son launukan Najeriya?
Sai abokin ya kada baki yana cewa kwarai ya san shi da jarabar, inda ya kara da cewa, ba zai yi mamaki ba idan ma aka ce launin dan-kamfai dinsa ma suna da launin kore da fari.
Wani armashi a kan wannan ma, ko rigunan wayoyinsa guda biyu dukkaninsu suna da launin kore da fari ne.
Ko shakka babu, babbar dama ce samun yin tozali da mutum mai karamci ga baki kuma dan kishin kasa irin Dokta Wandali. Sam babu wani abin mamaki da ake kiran sa da Mista Najeriya ko kuma Mista Green, White, Green, sannan yana son daga likkafar Najeriya. Komai nasa a kan Najeriya ne daga launukan kasar da al’adu da dabi’unta.
Babu shakka yadda mutane ire-irensa suka yi karanci; cike da kaifin basira da tawali’u da tausayi da suka zama abin buga misali kuma abin koyi, idan ana maganar kauna da kishin kasa saboda yadda suke sanya kyakkyawar fata ta yiyuwar samun makoma mai kyau ga Najeriya.
Kyakkyawar fatansa da burinsa da ma kwarin gwiwarsa ga Najeriya, sun sha gaban misali. Lura da wadannan dalilan suka dace a karfafe shi sannan a ba shi karfin gwiwa ta hanyar saka masa da lambar yabo daga hukumomin da abin ya shafa.
Allah Ya albarkaci kasarmu, Najeriya, Amin summa amin.
Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) mni fnipr, shi ne Sarkin Yakin Kanwan Katsina kuma tsohon Kakakin Rundunar Sojan Najeriya. Yana aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a kuma mazaunin Abuja.