Kida na rage wa yara radadin cutar daji a benezuela

Ana amfani da kida a asibitin kasar benezuela don saukaka wa kananan yara zafi da radadin ciwon daji. Wata yarinya ’yar shekara tara bictoria Alzuru tana cike da farin ciki kafin a yi maganin sarrafa sinadarai na ciwon daji, domin ta iya sarrafa garayarta, inda kida ke sanyawa ta manta da ciwon da ke damunta.Wannan […]

Kida na rage wa yara radadin cutar daji a benezuela
Kida na rage wa yara radadin cutar daji a benezuela

Ana amfani da kida a asibitin kasar benezuela don saukaka wa kananan yara zafi da radadin ciwon daji. Wata yarinya ’yar shekara tara bictoria Alzuru tana cike da farin ciki kafin a yi maganin sarrafa sinadarai na ciwon daji, domin ta iya sarrafa garayarta, inda kida ke sanyawa ta manta da ciwon da ke damunta.
Wannan yarinya da ke fama da cutar daji ta bayyana cewa zakin kida na debe mata kewa daga damuwa, kafin ta shiga wurin magani, a ciwon da ya cinye mata mahaifa. “Yana sanyawa ta mance da komai,” a cewar mahaifiyarta Lourdes ’yar shekara 43, wadda ke kai bictoria zuwa asibitin yara da ke birnin Caracas a kowane makonni biyu, inda take tashi daga gidansu da ke Los Tekues a Jihar Arewacin Miranda.
A kasar benezuela an bullo da darasin kida don warkar da yara, don haka a karkashin wani shiri na kasa, al’umar kasar ke kiransa da “El Sistema.” Kuma an shafe shekaru da dama ana gudanar da shirin, don ceto yara daga talauci da aikata miyagun laifuka, ta hanyar ba su ilimin sarrafa kida. A wadannan ’yan shekarun an fadada shirin zuwa asibitoci da cibiyoyin tsare masu laifi da matsugunnar marasa galihu.
Asibitin JM de los Rios shi ne na farko wajen rungumar shirin sarrafa kida na El Sistema. Yara na daukar darussan ne a lokacin da suke kwance a gadon asibiti, kafin a yi musu maganin cutar daji, ta hanyar sarrafa sinadarai na “chemotherapy.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan