Kidan gurmi sana’a ce ta farin jini da bakin jini – Shu’aibu Maigurmi
Wani fitaccen mai kidan gurmi da ke zaune a Jihar Legas mai suna Shu’aibu Maigurmi ya ce kidan gurmi sana’a ce ta bakin jini da kuma farin jini.Shu’aibu mai kimanin shekara 45 ya ce sha’awa ce ta sa ya bar sana’ar fawa ya koma kidan gurmi, sannan lokacin da yake sana’ar fawa ba ya samun […]

Wani fitaccen mai kidan gurmi da ke zaune a Jihar Legas mai suna Shu’aibu Maigurmi ya ce kidan gurmi sana’a ce ta bakin jini da kuma farin jini.
Shu’aibu mai kimanin shekara 45 ya ce sha’awa ce ta sa ya bar sana’ar fawa ya koma kidan gurmi, sannan lokacin da yake sana’ar fawa ba ya samun kudi kamar yadda yake samu a kidan gurmi.
Ya ce a dalilin kidan gurmi aka ba shi mota da katafaren fili a Legas. Ya hadu da manyan mutane da dama, yakan samu dubu 50 a lokaci daya ko fin haka.
Ya ce duk da kudin da yake samu a kidan gurmi bai sa ya dogara da shi ba, inda yake hadawa da sayar da gwanjo da dabino da turare da zannuwa. Duk da cewa wani lokaci yakan taba sana’ar fawa.
“Za ka ga wadansu masu kidan gurmi ba sa iya yin waka sai dai kida, wadansu kuwa ba sa iya yin kida sai dai waka, amma ni Allah ya hada mini gaba daya. Nakan yi kida in yi waka a lokaci guda ba tare da wata matsala ba.” In ji shi.
Ya ce ya shafe shekara fiye da 25 yana kidan gurmi, amma matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya ita ce irin yadda mutane suka dauki sana’ar a wulakance.
“Shi ya sa nake so Allah Ya raba ni da sana’ar nan, domin ita sana’ar roko sana’a ce ta bakin jini kuma sana’a ce ta farin jini. Wani lokaci mutane su raina ka wani lokaci kuma su girmama ka. Domin shi maroki babu inda ba zai iya shiga ba. Ba na fatan ’ya’yana su gaje ni a sana’ar roko, na fi son su gaje ni a sana’o’i na daban” inji shi.
Ya ce ya yi wakoki masu yawa kamar wakar ‘Sarkin Hadeja’ da ta ‘kauraye’ da ta ‘Usaini Jikan Boka’ da sauransu.