Kidan kokawa ya fi sata – Idiris Cali

Wani fitaccen mai kidan kokawa a Jihar Legas, mai suna Idiris Cali, ya ce ya tsunduma cikin kidan kokawa ne saboda ya samu rufin asiri. Makadin, dan shekaru fiye da 50 a duniya dan asalin kasar Nijar ne da ke zaune a yankin Mil 12 da ke Legas, ya bayyana wa Aminiya a karshen makon […]

Kidan kokawa ya fi sata – Idiris Cali
Kidan kokawa ya fi sata – Idiris Cali

Wani fitaccen mai kidan kokawa a Jihar Legas, mai suna Idiris Cali, ya ce ya tsunduma cikin kidan kokawa ne saboda ya samu rufin asiri.

Makadin, dan shekaru fiye da 50 a duniya dan asalin kasar Nijar ne da ke zaune a yankin Mil 12 da ke Legas, ya bayyana wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa kidan kokawa ya fi sata.
Ya ce: “Wannan kidan da nake yi ya rufa mini asiri domin nakan samu kudin da nake ciyar da iyalina, na yi sauran bukatun rayuwa na yau da kullum. Ka ga ke nan ya fi ka je ka saci kayan wani. ’Yan kokawar da nake yi wa kida sukan ba ni kyaututtuka na kudi da sutura kuma babu inda ban je ba. Na je garin Onisha da Fatakawal da Aba. Na je gabas da yamma, kudu da Arewa. Na yi yawo garuruwa da birane daban-daban.”
Ya ci gaba da cewa: “Da ni dan kokawa ne, na dade ina yin ta a kasarmu Nijar amma daga bisani da na ga karfina ya kare sai na kama kidan kokawa don na rika samun dan abin da zan rika cin abinci. A lokacin da nake kokawa na kayar da manyan ’yan kokawa da dama kuma na samu nasarori masu yawa.”
Ya bayyana cewa kidan kokawa da yake yi ba gada ya yi daga wurin iyayensa ba amma ya fi wanda ya gada iyawa.
“Ni ba gado na yi ba, rana tsaka na shiga kidan kokawa. Kuma ko wanda ya gada ba zai nuna mini komai ba sai ma na koya masa yadda ake yin kidan. Na samu rufin asiri sosai don ba na zuwa na ci bashi daga wurin jama’a.” Inji shi.
Ya kara da cewa burinsa shi ne dansa da yake yin sana’ar tare da shi ya gaje shi ya zama fitaccen mai kidan kokawa a duniya. dan nasa da yake taya shi kidan kokawa mai suna Gambo ya ce yana jin dadin gadon kidan kokawa da ya yi daga wurin mahaifinsa.
Gambo dan kimanin shekaru 30 a duniya ya ce abin da ba zai taba mantawa da shi ba a rayuwarsa shi ne, yadda wani dan kokawa ya kashe abokin hamayyarsa.
“Mun taba zuwa Maiduguri aka yi wata kokawa, sai aka yi nasara a kan wani dan kokawa sai abokin hamayyarsa ya tayar da rikici ya ce bai yarda ba; an yi masa rashin adalci. Bayan an tashi sai ya kama shi da fada har ta kai ya buga masa ice, nan take ya mutu. Gaskiya ba zan taba mantawa da wannan ba a rayuwata ba.” Inji shi.