Kifi mai fuskar mutum na korar mutane a kogi

Wani kifi mai fuska irin ta mutum ya tada kura a shafukan sada zumunta na zamani bayan an wallafa bidiyon kifin wanda ke yawo a cikin ruwa a hankali kamar mutum ya duka, saboda yanayin fuskarsa. Kwanan ne aka samu rahoton fuskar wani kare da take kama da ta mutum. Karen mai suna Nori, ya […]

Kifi mai fuskar mutum na korar mutane a kogi

Wani kifi mai fuska irin ta mutum ya tada kura a shafukan sada zumunta na zamani bayan an wallafa bidiyon kifin wanda ke yawo a cikin ruwa a hankali kamar mutum ya duka, saboda yanayin fuskarsa.

Kwanan ne aka samu rahoton fuskar wani kare da take kama da ta mutum. Karen mai suna Nori, ya sa jama’a da dama na ta tafka muhawara a shafukan Intanet inda wadansu ke zargin cewa, ko an hada hotunan da ya yi kama da na mutum ne.

Daga bisani sai ga wani kifi da shi kuma yake rayuwarsa a cikin ruwa. Wannan kifi dai an same shi ne a wani kogin kasar China, da yake dauke da wata fuskar mai ban al’ajabi kamar ta mutane.

Wani bako da ya ziyarci birnin Kunming a Kudancin China ne ya dauki bidiyon kifin wanda ya rika bai wa jama’a tsoro saboda yadda yake ninkaya a cikin kogin. Bakon ya wallafa shi ne a shafinsa na sada zumunta na Weibo da kasar China ke amfani da shi. Ana kallon kifin yana tasowa saman ruwa da fuska irin ta mutum.

A fuskar kifin akwai alamar digo kamar idanun mutum da kuma wata alama kamar zanen hanci da siffar baki irin ta mutane.

A cikin bidiyon an ji muryar wata mata na cewa, “Wannan kifin yana da siffar mutum.”

Yayin da wadansu jama’a suke maida martani a kan sha’awar nikayar kifin.

Wani kuwa cewa ya yi, “Wannan abin tsoro ne!”

Sannan wani ya ce,: “Wa yake da kwarin gwiwar cin wannan kifi?”

Daga bisani wani ya wallafa bidiyon kifin a shafin Tiwita na @Unedplained lokacin da yake motsi.

Wadansu dai na kallon kifin kamar ba mai rai ba, kamar labarin wani kifi Shark  da aka yi fim dinsa a shekarar 2014.

Wannan shi ne karon farko da aka taba samun kifi mai fuska irin ta mutum.