Kifi mai tsawon inci 7 ya makale wa masunci a makogwaro
Wani matashi mai shekara 24 mai sana’ar kamun kifi ya tsalleke rijiya da baya bayan wani kifi ya makale masa a cikin makogwaro.
Wani matashi mai shekara 24 mai sana’ar kamun kifi ya tsalleke rijiya da baya bayan wani kifi ya makale masa a cikin makogwaro lokacin da ya hadu da tsautsayi yayin kama kifin.
Kafar labarai ta kasar Kwalombiya ta wallafa wani rahoto kan wani matashi dan kasar daga yankin Pivijay cewa ya yi kusan rasa ransa yayin kama kifin.
- Zaben 2023: Jonathan ba ya cikin lissafin APC —Buni
- Sojoji sun hallaka kwamandojin Boko Haram 2 da ake nema ruwa a jallo a Borno
Matashin wanda aka sakaya sunansa, rahoto ya ce masunci ne da ke sana’ar su don kula da iyalansa, inda a ranar 23 ga Janairun bana ya yi kokarin kama kifin.
Yadda abin ya faru
Bayan ya cire kugiyar da ya kifayen, sai ya fahimci cewa akwai wani kifin da ya makale a wani bangare komar kama kifin.
Sai masuncin ya kama wanda yake son kufce masa ya rike da hakoransa hakan ya sa kifin ya zille ya shige cikin makogwaronsa yayin da yake kokarin nade wata kugiyar.
A cewar rahotannin da aka wallafa a kasar masuncin bai rike kifin da hakoransa da kyau ba.
Hakan ya bai wa kifin damar kufcewa zuwa cikin makogwaronsa. Kifin da masuncin ya hadiye na daya daga cikin jinsin kifayen da ake kira Mojarra, sai dai bai yi saurin shakar iska ba ta yadda zai yi wa masuncin illa.
Rahotan ya kara da cewa, bayan kifin ya makale wa masuncin ya kai kansa asibitin Santander Herrera.
Sai dai ya kasa yi wa likita bayanin abin da ya faru saboda bai iya yin numfashi, inda ya rika nuna makogwaronsa.
Kuma da aka yi hoton makogwaron ne aka gano abin da ke cikinsa inda aka tabbatar da cewa kifi ne ya makale a ciki.
An ciro kifin ta hanyar taimakon gaggawa da jami’an lafiya suka gudanar, sun ce ba a cika samun irin wannan hatsari ba.
Masuncin ya yi jinyar kwana biyu daga bisani aka sallame shi bayan samun lafiya.
A wani bidiyo da aka wallafa daya daga cikin likitoci ya ce: “Jama’a maza da mata wani abin mamaki ya faru, wani matashin masunci daga garin Pivijay ya haxiyi kifi da ransa.
Mun yi nasarar ciro shi daga cikin makogoronsa.” Irin wannan lamari ya taba faruwa inda wata kafar labarai ta kasar Masar a watanni kadan da suka gabata ta ce, an samu wani masunci da ya hadiyi irin wannan kifin.