KILAF: A Kano za a yi baje kolin fina-finan harsunan Afirka na 5

Shirye-shirye sun yi nisa na fara bikin bajen kolin fina-finan da ake yi da harsunan Afirka karo na farko tun bayan bullar COVID-19.

KILAF: A Kano za a yi baje kolin fina-finan harsunan Afirka na 5

Shirye-shirye sun yi nisa na fara bikin bajen kolin fina-finan da aka yi da harsunan Afirka karo na farko tun bayan bullar COVID-19.

Bikin, wanda shi ne karo na biyar, za a yi shi ne a birnin Kano daga ranar 24 zuwa 27 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Wanda ya shirya bikin, Abdulkreem Mohammed, ya shiada wa Aminiya cewa, taron na kwana uku ya zo da shirye–shirye da kuma abubuwa daban-daban.

Abubuwan sun hada da taron kara wa juna sani tare hadin gwiwar Jami’ar Bayero, tarukan horaswa kan rubutun fim da kasuwancinsu da kuma zayyana da kirkira.

Akwai kuma cin abinci da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a ranar farkon taron, sai kuma wata liyafar cin abincin dare da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, bayan an zagaya da mahalarta taron wuraren ban sha’awa da na tarihi na birnin Kano.

Kawo yanzu, baki daga kasashen Afirka takwas sun shigo da fina-finai 80 da za su yi gogayya don zama zakara a fannoni daban-daban.

Alkalan da za su fitar da gwani a fina-finan, an zabo su ne daga ciki da kuma wajen masana’antar Kannywood, karkashin  jagorancin Shugaban Kungiyar Daraktocin Fina-finai ta Kasa (DGN) Dokta Victor Okhai.

Daga Kannywood kuwa, akwai Shehu Daneji, tsohon marubuci kuma wanda ya nadawa masana’antar suna da kuma Mohammed S. Bello, darkata, mai horasa da jarumai, kuma mai suddabarun kwalliya.

Taron zai bayar da wata babbar dama ga ’yan Kannywood su yi cudanya da takwarorinsu na kasashen waje da kuma kyautata alaka.

Sannan na iya iya zama wata dama ta bunkasa yawon bude ido da kuma tallata Jihar Kano da harshen Hausa da Hausawa.