Kim Kardashian ta yi zanen tattoo a cikin bakinta a karon farko

Babu wani shiri da zan yi ba tare da na yi zanen tattoo ba.

Kim Kardashian ta yi zanen tattoo a cikin bakinta a karon farko

Fitacciyar ’yar kwalliyar nan wadda ta sauya halittarta ta hanyar yi wa fatar jikinta tiyata don nishadantar da magoya bayanta, Kim Kardashian ta ce ta yi zanen tattoo a asirce shekaru biyu da suka gabata, bayan wata rawar da ta taka wajen sauya fatar jikinta.

A cikin sabon shirin fim dinta, Kardashian mai shekara 43, ta bayyana tambarin zanen tattoo da ta yi, wanda ta boye a cikin bakinta.

Kim ta bude lebenta na kasa inda ta nuna zanen da ta yi wanda akasari ake yi a fatar jiki.

Ta ce, “Wani abu da ba ku sani ba game da ni shi ne. ‘Alama ce marar iyaka. ‘A bikin da ake shiryawa na SNL, lokacin da na halarci bikin SNL, ni da duk abokaina mun samu yin zanen tattoo masu dacewa.

“Kowa ya samu yin irin nasa kuma na kasance kamar babu wani shiri da zan yi ba tare da na yi zanen tattoo ba.

“Wannan shi ne yadda muke bikin da ake shiryawa a ranar Asabar da daddare na SNL, tare da yin karamin tattoo da safe,” in ji ta, tana cewa zafin yin zanen ba komai ba ne.

Labarin tattoo na iya zo wa mutane da yawa cikin mamaki yayin da tauraruwata ke haskawa a baya, lamarin da Kim ta bayyana “cewa zan samun kwarin gwiwa nan gaba.”

Kim Kardashian ta kasance tana sha’awar motar alfarma kirar Ferrari don ta kece-raini a tsakanin sa’o’inta

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa