King Kazu: Dan shekaru 56 da ke buga kwallo ya kafa tarihi
A yanzu haka ‘King Kuza yana kulob din Oliveirense ta kasar Poturgal.
“ Gemu” inji masu iya magana, “ba ya hana wasa, sai in wasan bai kama ba.” Hakan ce ta tabbata a kan wani dan wasan kwallon kafa wanda ya kai tsufansa na shekara 56 da haihuwa bai daina wasan kwallo ba, a inda a yake buga wa manyan kulob-kulob na duniya.
Miurashura Kazuyoshi dan kasar Japan shi ne mutumin da ya yi wannan baiwa, ya kuma soma wasan kwallon kafa tun yana saurayi da jajayen sawunsa har ya girma ya kai shekarun tsufa bai daina ba kuma hakan ta sa ya yi fice.
- APC ta bayar da ratar fiye da kuri’u dubu 200 a Zaɓen Gwamnan Kogi
- Angon da aka yi wa auren gata a Kano ya zargi surukansa da neman raba auren
Miura wanda ake yi wa lakabi da sarkin kwallo wato ‘King Kazu’ an haife shi a shekarar 1969 ya kuma kwallafa ransa a buga kwallon kafa a inda barinsa makaranter sakandare ke da wuya sai ya kaura zuwa kasar Brazil yana dan shekara 15 a inda ya samu shiga inda ke bayar da horo a wasan kwallo na Akadami.
Ya kuma samu ya buga wa wasu kulob-kulob kwallo a kasar kafin ya dawo gida Japan ya kuma daga martabr kwallon a kasar a inda ya shigo wasu kungiyoyi na gida ya kuma ciwo musu a gasa daban-daban, kafin ya tafi aro zuwa kasashen Italy da Croatia da Pakistan da kuma Australia a inda ya buga wa kulob-kulob din da suka samu nasara a wasanninsu.
Sai dai maimkon ya yi ritaya kamar sauran ‘yan wasan da suka doshi shekaru 30 da hahuwa, sai ma daura damara ya ci gaba da wasa a kulob din kasar ta Yokohama FC a inda ta dauke shi yana dan shekara 35.
Wanda zuwansa kulob din ya sa ta daga a gasar lig da ake yi daga kasa zuwa saman tebur.
Wannan kokari da kuma mayar da kai na Miura gami da yawan shekarunsa ta sa ya shiga kudin Guinness na abubuwan bajinta na duniya a matsayin dan kwallon da ya fi kowa tsufa yana wasa a duniya.
Kididdiga ta nuna ya buga kimani jimillar wasa 623 ya kuma zura kwallaye 180 a raga ya kuma lashe Kofi 15 a shekara 2021 kadai.
A yanzu haka ‘King Kuza yana kulob din Oliveirense ta kasar Poturgal a inda ta sabunta kwantiraginsa na buga mata kwallo na shekarun da babu adadi.