Kira ga al’ummar Najeriya
Ina mai fatan alheri da samun damar amfani da wannan kafa don isar da kirana ga ’yan Najeriya.Dalilin wannan kira ga nawa shi ne, don al’umma su yi la’akari da yanayin da kasar nan ke ciki. kasar nan na bukatar hadin kan al’uma wuri guda, domin ceto ta daga hannun azzalumai, wadanda suka yi kaka-gida […]
Ina mai fatan alheri da samun damar amfani da wannan kafa don isar da kirana ga ’yan Najeriya.
Dalilin wannan kira ga nawa shi ne, don al’umma su yi la’akari da yanayin da kasar nan ke ciki. kasar nan na bukatar hadin kan al’uma wuri guda, domin ceto ta daga hannun azzalumai, wadanda suka yi kaka-gida da dukiyar jama’a.
Don haka ’yan Najeriya, mu hada kai wuri guda domin ganin a wannan lokacin mai kishin talakawa, wato Janar Muhammadu Buhari ya samu ragamar mulkin kasar nan a zabe mai zuwa.
Shi Janar Muhammadu Buhari ya riga ya nuna cewa talaka yake kauna kuma duk abin da zai yi, zai yi shi ne domin amfanin talakawa. Ya zama tilas ga ’yan Najeriya na kowane sashe, mu hada kai waje daya, don ganin azzalumai ba su sami hanyar tsayawa a kan mulki ba a zabe da ke zuwa.
Sanin kowane, da samun mulkin farar hula, shekaru kusan goma sha biyar ke nan amma abubuwa sai lalacewa suke yi. Yau wutar lantarki ta zama abin da ke tafiyar hawainiya, yau akwai gobe babu. Arzikin kasa ya zama a
hannu ’yan kalilan da ’yan shalelen gwamnati. Kuma sai mutum kamar Janar Muhammadu Buhari ne zai iya dakatar da cin hanci da rashawa da ya yi katutu a harkokin gudanarwa da aikace-aikacen gwamnati a Najeriya.
Don haka ya zama dole ga ’yan Najeriya da mu dubi Allah, mu dubi Annabi, mu hada kai domin ganin cewa wannan bawan Allah da ke kaunar talakawa ya samu hawa karagar mulki, don biya wa talaka bukatun more rayuwa.
Kiran da nake yi wa ’yan Najeriya shi ne, su gane cewa a yanzu talaka ba shi da wata mafaka sai dai ya tsaya ya tabbatar da cewa Janar ya samu ya zama Shugaban kasa kawai. Kuma hanya daya ce shi talakan zai yi amfani da ita. Ita wannan hanya ita ce, tsayawa ya tabbatar a zabe kuri’asa ta kirgu. Baya ga haka, shi talakan ya cire kwadayi da son abin hannun ’yan jari-hujja, wanda a lokacin za su iya ba shi komai amma daga baya zai yi kuka. Hausawa suna karin maganar cewa, hali zanen dutse. Halin ’yan jari-hujja shi ne su saka shi talaka cikin wahala sosai.
Don haka ’yan Najeriya, komai na hannuku, sai abin da kuka yi, ku samar wa kanku ’yanci. Ta wadannan hanyoyin ne kawai ’yan Najeriya za su cin ma bukatar ganin mai son su ne ke shugabancin kasarmu. Jiki dai magayi ne, kamar yadda masu iya magana suka ce.
Maiyadi ya aiko daga Jimeta-Yola, Jihar Adamawa