Kira ga Gwamna Ambod
Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku miqa min roqona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin yadda darajar Bahaushe take zubewa saboda ’yan uwammu Hausawa da suke zubar mana da mutumci wajen barace-barace. Za ka ga mata da yara qanana suna yawo, ko kuma da jirirai suna nuna […]
Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku miqa min roqona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin yadda darajar Bahaushe take zubewa saboda ’yan uwammu Hausawa da suke zubar mana da mutumci wajen barace-barace. Za ka ga mata da yara qanana suna yawo, ko kuma da jirirai suna nuna bakinsu wai a ba su na abinci. Kuma wallahi har ma cikin shege ake yi musu yanzu. Don Allah Bahaushe da ke da daraja da kuma addinin Musuunci, ai addini bai ce mata da yara qanana a riqa xibarsu ana koya musu yawo zuwa jihohin Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu ba. Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji 08111389999, 08096368393
Mu koma ga Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas ko shakka babu mu al’ummar Arewacin Najeriya muna cikin wani halin da sai dai mu qara dagewa da roqon Allah, tare da gyara tsakanin mu da Allah, ta hanyar istigifari da hailala da salatin Annabi, ko zai kawo mana qarshen zubar da jinin bayin Allah. Ganin yadda wasu xauke da boma-bomai suka far wa al’ummar jihohin Adamawa da Kano, inda suka kashe jama’a da dama. Don haka muke kira ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro su xauki matakin ba sani, ba sabo ga duk wanda aka kama da hannu wajen zubar da jinin bayin Allah da kai hare-haren ta’addanci. A qarshe muke roqon Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a qasar mu baki xayanta, da ma qasashe makwabtan mu. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999/ 08138203747 [email protected]
A kashe wuta lokacin hunturu
Assalam. Edita, lallai yanzu mun shiga lokacin sanyi, mu kula da yara masu hura wuta, don jin xumi da zarar sun gama su kasheta. Haka mutanen qauyuka su ma su sa ido akan duk mai hura wuta don kiyaye gidajensu,wanda mafi yawa qirare ne da manoma suka yi qoqarin kwashe amfanin gonakansu, don gudun fataken dare, da aukawar makiyaya gonakinsu. Daga Hussaini Almusaya Gombe, 08130446601
Gargaxi ga ’yan majalisa
Aminiya ’yar amana don Allah ki miqa min saqona ga ’yan majalisun qasa da su sani rigar Shugaba Buhari suka shiga, suka ci zave, amma suna nema su kauce daga tsarin da yake so ya sa qasar nan a gaba. To, su sani shekarar 2019 na zuwa, mu talakawa muna jiransu. Daga Musa Unguwar Maiyasin da Rabi’atu Xanja Jihar Katsina 08060611124 08069274090
Ta’aziyya ga Kano da Yola
Assalamu alaikum, Edita ka isar da saqona ga al’ummar Kano da na Yola Jihar Adamawa, bisa rayukan da aka rasa a jihohin dalilin harin bom da aka kai musu, wanda qungiyar ta’adancin suka kai musu. Allah ya jiqan waxanda suka rasu, Ya bai wa waxanda suka jikkata lafiya. Daga Bilya Tukur Bakori 09033272527 [email protected]
Ta’aziyyar Prince Audu
Haqiqa mutuwa rigar kowa. Qungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina na yin ta’aziya ga iyalai da ’yan uwa da abokan arzika da masoya da Jam’iyar APC da kuma Gwamnatin Jihar Kogi bisa ga rasuwar Prince Abubakar Abdu. Da fatan Allah Ubangiji Ya jiqansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Allah Ya sa mu cika da imani. Daga Haruna Muhammad Katsina. [email protected] 07039205659
Jinjina ga jam’iyyar APC
Salam Aminiya Hausa. Jinjina ga jam’iyyar APC ta qasa kan yin nazari da zaven da aka gudanar a jihar Kogi wanda Allah ya yi wa xan takarar Jam’iyyar APC marigayi Alhaji Abubakar Audu rasuwa da fatan za su yi nazari bisa adalci da Gaskiya. 08108003333. [email protected]
Ta’aziyyar Aja Gwarzo
Haqiqa mutuwa rigar kowa. Muna yin ta’aziya ga iyalai da ’yan’uwa da abokan arzika da Hukumar gidan rediyo Najeriya ta Kaduna (FRCN), bisa ga rasuwar Alhaji Ahmad Aja Gwarzo Mai gabatar da shirin Wasa Qwaqwalwa da kuma sanarwa.Da fatan Allah Ubangiji Ya jiqansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Ya sa mu cika da imani. Daga Qungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina. 07039205659
Ta’aziyyar Prince Audu
Rai Baqon Duniya. A yau cikin alhini ina miqa saqon ta’aziyyata zuwa ga ‘yan uwa da iyalan marigayi xan takarar gwamnan jihar Kogi wato Alhaji Abubakar Audu. A gaskiya an yi babban rashi sabili da mutuwa ta yi wa Audu zuwan ba- zata. A vangare guda kuma ina mai jan hankalin ‘yan siyasar Najeriya da su koyi darasi da mutuwar Prince Audu sabili da mutuwa ba ta da sa’i. A qarshe muna addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya sa ya huta mu kuma da muke raye Allah Ya sa mu yi kyakkyawan qarshe amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, Jihar Borno. 09091513043
Ta’aziyyar Prince Audu
Assalamu Alaikum Edita ku ba ni dama in miqa saqon ta’aziyya ga xaukacin al’ummar Jihar Kogi dangane da rasuwar Marigayi Alhaji Prince Abubakar Audu zavavven Gwamnan Jihar Kogi, kuma xan takar jam’iyyar APC. Da fatan Allah Ya jiqansa da rahama, Ya sa kwanciya hutu ce ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannnan babban rashi, mu kuma da muka yi saura idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani amin. Daga Mohammed Maikaset Cross Kauwa Qaramar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. mohammedmaikaset120@yahoo, [email protected] 08138775015.
Kira ga Gwamna Ganduje
Aminiya ku gaya wa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya yi watsi da masu yin maganganun banza, ya sa Jihar Kano gaba, wajen ci gaba da ayyukan da ya gada da kuma wanda zai xora. Masu waxannan maganganu ba aikin ba ne gaban su, sai dai aljihunsu da ya yi qasa sai su shiga kafafen yax a labarai su yi ta faxar abin da suka ga dama. Daga [email protected]
Kira ga Gwamna Ambode
Salam. Aminiya ina so ku taimake ni ku mika min rokona ga Gwamna Akinwumi Ambode da ya hana barace-barace a Jihar Legas. Domin yadda darajar Bahaushe take zubewa saboda ’yan uwammu Hausawa da suke zubar mana da mutumci wajen barace-barace. Za ka ga mata da yara kanana suna yawo, ko kuma da jirirai suna nuna bakinsu wai a ba su na abinci. Kuma wallahi har ma cikin shege ake yi musu yanzu. Don Allah Bahaushe da ke da daraja da kuma addinin Musuunci, ai addini bai ce mata da yara kanana a rika dibarsu ana koya musu yawo zuwa jihohin Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu ba. Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Sha’aibu mile 12 Legas 08111389999, 08096368393
Mu koma ga Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas ko shakka babu mu al’ummar Arewacin Najeriya muna cikin wani halin da sai dai mu kara dagewa da rokon Allah, tare da gyara tsakanin mu da Allah, ta hanyar istigifari da hailala da salatin Annabi, ko zai kawo mana karshen zubar da jinin bayin Allah. Ganin yadda wasu dauke da boma-bomai suka far wa al’ummar jihohin Adamawa da Kano, inda suka kashe jama’a da dama. Don haka muke kira ga gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaro su dauki matakin ba sani, ba sabo ga duk wanda aka kama da hannu wajen zubar da jinin bayin Allah da kai hare-haren ta’addanci. A karshe muke rokon Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya a kasar mu baki dayanta, da ma kasashe makwabtan mu. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999/ 08138203747 [email protected]
A kashe wuta lokacin hunturu
Assalam. Edita, lallai yanzu mun shiga lokacin sanyi, mu kula da yara masu hura wuta, don jin dumi da zarar sun gama su kasheta. Haka mutanen kauyuka su ma su sa ido akan duk mai hura wuta don kiyaye gidajensu,wanda mafi yawa kirare ne da manoma suka yi kokarin kwashe amfanin gonakansu, don gudun fataken dare, da aukawar makiyaya gonakinsu. Daga Hussaini Almusaya Gombe, 08130446601
Gargadi ga ’yan majalisa
Aminiya ’yar amana don Allah ki mika min sakona ga ’yan majalisun kasa da su sani rigar Shugaba Buhari suka shiga, suka ci zabe, amma suna nema su kauce daga tsarin da yake so ya sa kasar nan a gaba. To, su sani shekarar 2019 na zuwa, mu talakawa muna jiransu. Daga Musa Unguwar Maiyasin da Rabi’atu danja Jihar Katsina 08060611124 08069274090
Ta’aziyya ga Kano da Yola
Assalamu alaikum, Edita ka isar da sakona ga al’ummar Kano da na Yola Jihar Adamawa, bisa rayukan da aka rasa a jihohin dalilin harin bom da aka kai musu, wanda kungiyar ta’adancin suka kai musu. Allah ya jikan wadanda suka rasu, Ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya. Daga Bilya Tukur Bakori 09033272527 [email protected]
Ta’aziyyar Prince Audu
Hakika mutuwa rigar kowa. kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina na yin ta’aziya ga iyalai da ’yan uwa da abokan arzika da masoya da Jam’iyar APC da kuma Gwamnatin Jihar Kogi bisa ga rasuwar Prince Abubakar Abdu. Da fatan Allah Ubangiji Ya jikansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Allah Ya sa mu cika da imani. Daga Haruna Muhammad Katsina. [email protected] 07039205659
Jinjina ga jam’iyyar APC
Salam Aminiya Hausa. Jinjina ga jam’iyyar APC ta kasa kan yin nazari da zaben da aka gudanar a jihar Kogi wanda Allah ya yi wa dan takarar Jam’iyyar APC marigayi Alhaji Abubakar Audu rasuwa da fatan za su yi nazari bisa adalci da Gaskiya. 08108003333. [email protected]
Ta’aziyyar Aja Gwarzo
Hakika mutuwa rigar kowa. Muna yin ta’aziya ga iyalai da ’yan’uwa da abokan arzika da Hukumar gidan rediyo Najeriya ta Kaduna (FRCN), bisa ga rasuwar Alhaji Ahmad Aja Gwarzo Mai gabatar da shirin Wasa kwakwalwa da kuma sanarwa.Da fatan Allah Ubangiji Ya jikansa da rahama. Mu da muke jiran namu lokacin Ya sa mu cika da imani. Daga kungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina. 07039205659
Ta’aziyyar Prince Audu
Rai Bakon Duniya. A yau cikin alhini ina mika sakon ta’aziyyata zuwa ga ‘yan uwa da iyalan marigayi dan takarar gwamnan jihar Kogi wato Alhaji Abubakar Audu. A gaskiya an yi babban rashi sabili da mutuwa ta yi wa Audu zuwan ba- zata. A bangare guda kuma ina mai jan hankalin ‘yan siyasar Najeriya da su koyi darasi da mutuwar Prince Audu sabili da mutuwa ba ta da sa’i. A karshe muna addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya sa ya huta mu kuma da muke raye Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, Jihar Borno. 09091513043
Ta’aziyyar Prince Audu
Assalamu Alaikum Edita ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’ummar Jihar Kogi dangane da rasuwar Marigayi Alhaji Prince Abubakar Audu zababben Gwamnan Jihar Kogi, kuma dan takar jam’iyyar APC. Da fatan Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa kwanciya hutu ce ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannnan babban rashi, mu kuma da muka yi saura idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani amin. Daga Mohammed Maikaset Cross Kauwa karamar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. mohammedmaikaset120@yahoo, [email protected] 08138775015.
Kira ga Gwamna Ganduje
Aminiya ku gaya wa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya yi watsi da masu yin maganganun banza, ya sa Jihar Kano gaba, wajen ci gaba da ayyukan da ya gada da kuma wanda zai dora. Masu wadannan maganganu ba aikin ba ne gaban su, sai dai aljihunsu da ya yi kasa sai su shiga kafafen yad a labarai su yi ta fadar abin da suka ga dama. Daga [email protected]