Kira ga gwamnati kan kalubalen tsaro a Najeriya
Abubuwan da ya kama ta a yi don magance matsalar tsaro a Najeriya.
Najeriya babbar kasa ce a Yammacin Afirka, wacce Allah Ya albarkace ta da tarin ni’imomi da albarkatu masu yawa, kama daga yawan jama’a da suka haura miliyan 200, da kuma ma’adinan karkashin kasa, na ruwa da na kan tudu, wadanda ba kowace kasa ce Allah Ya bai wa wannan arzikin ba.
Sai dai kuma kalubale iri-iri sun dabaibaye ta, da suka hada da rashin shugabanci nagari, cin hanci, kabilanci da bangaranci, da kuma uwa uba matsalar tabarbarewar tsaro.
- An kama sojan sama kan zargin shi da hannu a harin NDA
- Gasar hoto ta Daily Trust/Aminiya: Sharuddan shiga gasar:
Duk da kokarin da masu rike da madafun iko, kwararru da rundunonin tsaron kasa suke cewa suna yi don shawo kan wadannan matsaloli da suka dabaibaye kasar nan, har yanzu haka ba ta cim-ma ruwa ba.
’Yan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin kunci da talauci, harkokin tafiyar da gwamnati sai kara lalacewa suke yi saboda rashin kishin kasa da ayyukan rashin gaskiya da suka yi yawa, ga kuma karuwar kungiyoyin ’yan ta’adda da tsageru da suka yi yawa a cikin kasa, suna haifar da firgici a zukatan ’yan Najeriya da asarar rayuka da dukiyoyi.
Lallai akwai bukatar hukumomi su tashi tsaye su tabbatar sun samar da sabbin dabaru da tsare-tsare a irin matakan da suke dauka, saboda rayuwa kullum kara sauyawa take yi, kuma su ma bata-gari canza salo da dabaru suke yi.
Daga cikin matakan da ya kamata a bi wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya sun hada da dakile cin hanci da rashawa.
Domin kuwa cin hanci da rashawa babbar hanya ce ta maganin matsalolin Najeriya, tun daga kan shugabanni har zuwa ga talakawa.
Sannan wajibi ne a karfafa tare da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri, saboda gano irin makarkashiyar da wasu bata-gari daga ciki da wajen kasar nan suke kokarin haddasawa ta hanyar amfani da wasu baragurbin ’yan kasa suna haifar da yamutsi nan da can, domin karkatar da tunanin hukumomi da jami’an tsaro wajen kunna wutar futintinun da ba za a gano tushensu da wuri ba, ballantana a samar da mafita.
Matukar aka yi kokari aka toshe wannan hanya to, lallai akwai kyakkyawan zaton za a samu saukin tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Har wa yau daga bangaren yadda jami’an tsaro ke amfani da ’yan jarida da kafofin sadarwa na zamani wajen yada farfaganda da kururuta ayyukan da suke gudanarwa, don jawo ra’ayin jama’ar kasa. Hakan yana da muhimmanci, amma kuma yana da hadari.
Magance matsalolin tsaro na bukatar sirri ne sosai da Kuma ƙwararrun ma’aikatan tsaro da sabbin dabaru.
Abin nufi a nan shi ne, dukkan wani aiki da aka shirya za a gabatar da shi bai kamata a yi ta yadawa a kafafen sada zumunta ba, saboda fitar da wannan sirri zai sanya wadanda za a kai wa samame ko farmaki, su sake sabon shiri.
Amma matukar aka bar al’amarin a cikin sirri hakika suna masu sakankancewa za a ci galaba a kansu. Babu shakka wannan ma hanya ce mai bullewa wajen magance matsalar tsaro.
Bisa la’akari da yawan jama’a da Allah Ya albarkaci kasar nan da shi, ya zama tilas ga hukumomi su magance wannan matsala, wajen samar da guraben ayyukan yi, domin dauke tunanin matasa daga shiga ayyukan da ba su kamata ba.
Yana da kyau wajen daukar ma’aikatan tsaro a tantance wadanda suke da kishin kasa kuma ba a san su da mummunar halayya ba, ba wai kawai a dinga dibar yara kara zube ko wadanda ke da gata da daurin gindin manyan kasa ba, wadanda babu abin da za su iya yi wa kansu sai sharholiya, da kara bata kasa.
Daga karshe muna fatan Allah Ya tabbatar mana da tsaro a kasarmu Najeriya, ya kuma ba mu lafiya da zaman lafiya baki daya.
Mannubiyya Abdulƙadir Mu’azu, marubuciya ce da ke zaune a Jos, Jihar Filato. [email protected]