Kira ga matasa
Edita, ina so a ba ni fili don na bayyana ra’ayina a game da yadda siyasar Najeriya ke tafiya a halin yanzu. A gaskiya yadda ba kasafai ake tsayar da talakawa musamman matasa a mukamai daban-daban a siyasar kasar nan ba abin akwai takaici. Za ka tarar mukamai da dama, ba a tsayar da talaka […]
Edita, ina so a ba ni fili don na bayyana ra’ayina a game da yadda siyasar Najeriya ke tafiya a halin yanzu. A gaskiya yadda ba kasafai ake tsayar da talakawa musamman matasa a mukamai daban-daban a siyasar kasar nan ba abin akwai takaici. Za ka tarar mukamai da dama, ba a tsayar da talaka sai masu kudi, da hakan ta sa ake mayar da abin kamar na gado.
Mu gane, yanzu fa kan mage ya waye, kuma kowane matashi yana da damar ya tsaya takarar kowane irin mukami kuma a zabe shi don shi ma ya sha romon dimokuradiyya.
Don haka ina kira ga matasa da sauran al’ummar Najeriya cewa tun da zaben 2019 yana karatowa yakamata a samu canji wajen ba matasa dama, don su ma a dama da su. Don mafi yawan mukaman da ake takarar a kansu za ka tarar tsofaffin ’yan siyasa ne ko kuma masu kudi ko masu daurin gindi, amma an bar matasa a baya idan sun tura mota sai ta tafi ta bar su suna cizon yatsa.
A wannan lokaci, ina kira ga daukacin matasa da su hada karfi da karfe wajen ganin sun kwatarwa kansu ’yanci ta hanyar tsayawa takara a mukamai daban-daban na siyasa don su ma a rika damawa da su.
Sannan ina kira ga matasa da su guji yin bangar siyasa, su daina bari ana amfani da su wajen kashe-kashe da kone-kone don biyan bukatar wasu. Su sani su ne manyan gobe, idan suka kuskura suka ci gaba da yin bangar siyasa, to su za a bari da cizon yatsa a gobe a lokacin da suka girma kuma al’amurra sun kwace musu.
Matasa ku dage wajen neman ilimi da aiki da shi, da yi wa na gaba biyayya da kuma neman halaliya ba lallai sai an tsaya ga aikin ofis ba.
Masu kasuwanci su rike kasuwancinsu, masu karatu su ci gaba da karatunsu sannan masu aikin karfi su ma su dage. Arziki dai nufin Allah ne, kuma Allah na azurta bawanSa ta inda bawan bai zata ba.
Da fatan matasa za su yi karatun ta-natsu kuma su yi amfani da wannan ’yar nasiha da na yi.
Mustapha Sa’idu Mohammed Anka
[email protected], 08037558407