Kira ga matasa

Salam, ’yan uwana matasa da sauran al’ummar Manzon Allah (SAW) da fatan muna cikin koshin lafiya. A yau na kuduri aniyar yin kira ne na musamman ga matasa a kan mu gyara halayenmu, mu yi abin da ya kamata, domin Hausawa na cewa ana gyara yau ne domin gobe. A kullum idan na shiga yanar […]

Kira ga matasa
Kira ga matasa

Salam, ’yan uwana matasa da sauran al’ummar Manzon Allah (SAW) da fatan muna cikin koshin lafiya. A yau na kuduri aniyar yin kira ne na musamman ga matasa a kan mu gyara halayenmu, mu yi abin da ya kamata, domin Hausawa na cewa ana gyara yau ne domin gobe.

A kullum idan na shiga yanar gizo, ko  na duba jaridu da mujallu sai in yi ta mamakin yadda matasa suke fafutika da rubuce-rubuce a kan lallai sai an ba mu ragamar mulki. Suna masu koken cewa ana danne mana hakki. Sannan  a wani bangaren idan na duba na ga yadda muke kumfar baki da zagin juna a kan abin da bai kai ya kawo ba, sai hankalina ya tashi. Shin irin wadannan matasan da suka zama ’yan bangar siyasa, suke zagin manya sannan uwa uba suke raina iyayensu ne za su zama shugabannin gobe? Allah wadaran naka ya lalace. Mene ne amfani badi ba rai? Ai ko da Annabi Muhammad (SAW) ya ce mu hayayyafa domin ya yi alfahara da mu a ranar gobe kiyama, ba mutanen banza yake nufi ba, yana nufin mutanen kirki ne wadanda suka san abin da yake musu ciwo, sannan kuma suka san inda za su je neman magani.

’Yan uwa matasa, ya kamata mu gane irin yaudarar da ake yi mana a fagen siyasa, wai yanzu ana cewa za mu iya tsayawa takara, ta ina zan tsaya takara? Da shekaru ake tsayawa takara ko da kudi? Me ya hada biri da gada?

Ya kamata mu gane, siyasar Najeriya ta kudi ce da masu kudi. Ba ta talaka ba ce ko dan talaka. Shi dan talaka sai dai su janyo mu kusa da su su yi amfani da mu wajen samun nasara, sannan su yi watsi da mu daga baya. Wannan rainin wayyo har ina? Sun hana mu samun ilimi mai nagarta, saboda suna so ’ya’yansu su mulke mu kamar yadda suka mulki iyayenmu. Asibitici sun zama tamkar wajen mutuwa saboda lalacewa. Komai  nasu daban, namu daban. A komai sai an bambanta tsakaninmu da su. A haka za mu ci gaba? Ina ka taba ganin dan wani shugaba mai rike da madafun iko ya fito ana bangar siyasa da shi? Kun san suna ina? Suna cikin daki suna shan iskar AC  suna kallonmu a talabajin ko a shafukan sada zumunta na zamani muna zagin juna, muna tozarta juna, wani lokacin muna yakar juna har ya kai ga kisa. Ko kuma suna can kasashen waje suna kallonmu. Wani lokacin ma su kalla su yi mana dariya. 

Idan ba ku sani ba, to ku sani yau. Sun shirya wannan shirin ne na cewa matasa ma za su iya tsayawa takara domin ’ya’yansu su fara tsayawa takara su ci gaba da mulkanmu ba wai don talaka ba. Ina fama da talauci da tunanin abin da zan ci, ina zan yi wani tunanin tsayawa takara? Ka ga ke nan idan har kudirin ya tabbata, ’ya’yan masu kudi ne za su tsaya takara su kara da iyayensu, mu kuma sai mu goya musu baya a ci gaba daga inda aka tsaya. Shi ke nan mun zama bayi. Kuma ina tabbatar muku cewa gara iyayen da ’ya’yan domin ko kadan ’ya’yan ba su da tausayi daidai da kwayar zarra, saboda ba su san talauci ba, son taso cikin jin dadi da more rayuwa. Ashe gara iyayensu da suka taso cikin talauci, domin ko ba komai, sun san talauci, kuma suna da dan tausayi. 

Na taba zantawa da wata yarinya, inda take mamakin cewa akwai gidan da ba su da motar hawa. Ni kuwa nake ce mata ba maganar motar hawa ake yi ba, akwai gidaje da yawa da abin da za a saka a bakin salati ma gagararsu yake yi.

Da haka ne na rubuta wannann takaitacciyar makala zuwa ga ’yan uwana matasa da mu gyara yadda muke tafiyar da al’amura. Mu daina zama ’yan amshin shata a wajen ’yan siyasa da wadansu mutanen banza. Abin ban haushi shi ne yadda har da masu ilimi suka shiga cikin irin wannan tsari na sakarci da tumasanci. Lokaci ya yi da za mu zama masu fada a ji a kasar nan, amma har yanzu mun ki nuna alamar cewa lokacin ya yi. Har yanzu manyan suna ci gaba da raina mana wayo saboda sun gane lagonmu.

A karshe nake fata za mu gyara. Mu zama masu kokarin neman ilimi na boko da na addini kuma mu kama sana’a. Mu zama masu ladabi da biyayya ga iyaye da sauran dattijan gari. Sannan mu zama masu hadin kai a tsakaninmu domin idan muka hada kai, ’yan siyasa ma za su fara jin tsoro. Allah Ya ba mu ikon yin gyara, domin idan mun gyara, mu ne za mu ci moriyar abin. Ai dama ana wanke tukunya ce domin gobe.  

Mukhtar Abdullahi ya rubuto wannan makala ce daga Hayin Banki Kaduna.  08060769255