Kira ga matasa a kan bangar siyasa
A duniyar dimokuradiyya babu abin da za a yi amfani da shi wajen yaudarar al’umma a wannan zamani face an danganta da rayuwar matasa, kasancewar babu wani buri da matashi ke bukata face ya ga ya tsinci rayuwarsa a cikin sauki da samun ingancin rayuwa ta hanyar dogaro da kai. Wajen neman saukin rayuwa ne ke […]
A duniyar dimokuradiyya babu abin da za a yi amfani da shi wajen yaudarar al’umma a wannan zamani face an danganta da rayuwar matasa, kasancewar babu wani buri da matashi ke bukata face ya ga ya tsinci rayuwarsa a cikin sauki da samun ingancin rayuwa ta hanyar dogaro da kai.
Wajen neman saukin rayuwa ne ke dulmiyar da mafi yawan matasa, kwadayi da gaggawar samun jin dadin ne ke kawo tabarbarewar rayuwarsu da samun damar wadansu ’yan siyasa su gurbatar da rayuwarsu cikin sauki, domin amfani da su wajen cin zarafin al’umma da tallar karya da ba su tarbiyyar rashin kishin kansu da kuma dagula musu rayuwa.
Yanzu lokaci ne na gudanar da kamfen din siyasa a Najeriya. Don haka ina kira ga ’yan uwana matasa mu hankalta, mu tuna iyayenmu da malamanmu da gidajenmu ne a zagaye da mu. Hasali ma babu mai son mahaifansa da ’yan uwansa su shiga cikin kuncin rayuwa ko halin ni-’yasu, in ko haka ne to ya kamata mu shiga taitayinmu wajen yakar miyagun dabi’un da muka aro daga dimokuradiyya mu kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma ta hanyar zaben shugabanni nagari wadanda ke da burin ganin mun zama manyan gobe.
Siyasa na da muhimmanci a kowacce kasa ta duniya da ke bin tafarkin dimokuradiyya. Dalili kuwa shi ne dimokuradiyya ce ke bai wa jama’a damar zabar wadanda suke ganin sun dace da su, kuma wadanda za su biya musu bukatunsu da kuma share musu hawaye. Jama’a kan ba da goyon baya ga wadanda suka yi imanin za su wakilce su kuma wakilci nagari ba wadanda za su je don wakiltar kansu ba.
Ta yaya jama’a za su tabbatar sun zabi shugabanni nagari ba zaben tumun-dare ba? Insha Allahu nan gaba kadan zan yi wa al’umma bayani a kan su wane ne ya kamata su zaba, amma yanzu ina so ne in yi kira ga ’yan uwana matasa a kan su guji bangar siyasa.
Tun bayan da Najeriya ta koma tsarin dimokuradiyya yau kusan shekara 20 ’yan siyasar kasar ke amfani da matasa domin cimma manufofinsu na siyasa. Ba laifi ba ne ’yan siyasa su nemi goyon bayan matasa. Abin da yake laifi shi ne amfani da matasa a matsayin ’yan bangar siyasa domin samun nasara a zabe.
A zabubbukan da suka wakana a baya ’yan siyasa a Najeriya na bai wa matasa kudi inda su kuma sukan sayi kwaya da sauran abubuwan sa maye da makamai suna bi suna razanar da abokan hamayya da sauran jama’a.
A kan yi fito-na-fito a tsakanin ’yan bangar siyasar. Wani lokaci ma a ji munanan raunuka, a wasu lokuta a rasa rayuka. Wannan abin takaici da me ya yi kama?
Shin matasan nan da suke bari ana amfani da su don cimma manufar zabe duk da cewa sun san ’yan siyasa za su yi watsi da su da zarar sun yi nasara, sun san ciwon kansu kuwa? Suna da masaniya cewa ’yan siyasa ba su damu da su ba illa kawai sun mai da su tamkar matattakala ce da suke takawa domin cin zabe ko ta halin kaka?
Amsar da nake bukata ita ce ta yaya matasa za mu jajirce mu ki yarda ana amfani da mu a matsayin ’yan bangar siyasa a kan kudi kalilan wadanda ake wa kallon marasa mutunci a Najeriya? Lamarin da ka iya sanadiyyar asarar rayukanmu da ci bayan kasarmu?
Tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowace al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwa sakaka. Wajibi ne da ya hau kan al’umma ta yi tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da sakonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su kaurace musu.
Duk wata kasa da ta ci gaba a wannan duniyar, idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar ci gaban, za a ga a hannun matasansu yake. Saboda ba su yi sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba.
Hakki ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye su kasance mataki na farko ta inda ’ya’yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane da kiyaye dokokin kasa da kauce wa ayyukan barna da sauransu.
Idan iyaye suka gaza aikata hakan ga ’ya’yansu, babu tantama a daidai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (matashi) ya fara mu’amala da wadansu abokai a waje, za su koya masa dukan dabi’un da suka ga dama. A wasu lokutan ma yanayin mu’amalar da ke tsakaninsa da su ne zai sa ya rika kwaikwayon yadda suke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina tasa dabi’ar.
Shekaru da dama muna ta addu’ar Allah Ya kawo mana shugabanni nagari a kasarmu, shekaru a baya iyayenmu suna ta cewa mu ne manyan gobe amma har yanzu ba mu da shugabanni masu tausayinmu, kuma har yanzu ba mu zama manyan goben ba.
To me ya jawo haka? Me ya sa har yanzu kasarmu ta kasa zama yadda muke fata kuma muke ta yi mata addu’a? Amsa ita ce mu matasa mun kasa fahimtar irin gudunmawar da za mu iya bayarwa domin kasarmu ta gyaru. Mun yi shiru mun kasa cewa uffan kan yadda barayi ke ta kwashe dukiyoyinmu, mun yi shiru mun kuma kasa haduwa wuri guda domin mu hada kai mu gyara kasarmu.
Ba komai yake sa ni takaici ba illa yadda matasa muka yi sakaci da harkar ilimi! Ga mu da yawan gaske amma ba mu da aikin yi sai kallon kwallo da tadin kwallo da kuma yawon bangar siyasa. Ga mu da yawan amma mun ki yarda mu nemi ilimi domin mu tallafa wa kasarmu.
Wannan shi ne dalilin da ya sa baragurbin ’yan siyasa wadanda ba burinsu ci gaban Najeriya ba suke amfani da mu wajen cimma mummunar manufarsu ta aika-aika. Su ne suke ba mu makamai da kwayoyi domin mu aikata abubuwan da suke so.
A karshe ina kira ga iyayye da sauran al’umma mu tashi tsaye wajen yi wa matasanmu da kasarmu addu’a.
Wassalam.
Mohammed Bala Garba ya rubuto ne daga Maiduguri.
08098331260.