Kira ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu
Hame da batun amincewa da gina sabbin kwalejojin Ilimi na gwamnatintarayya guda 6, wato (Federal College Of Education)da gwamnatin Najeriya ta yi, ciki har da (1) a jiharmu ta Bauchi hakika wannan babban ci gaba ne kuma abin a yaba, ganin cewa ilimi shi ne garkuwar dan Adam, kuma ilimi shi ne silar ci gaban […]
Hame da batun amincewa da gina sabbin kwalejojin Ilimi na gwamnatintarayya guda 6, wato (Federal College Of Education)da gwamnatin Najeriya ta yi, ciki har da (1) a jiharmu ta Bauchi hakika wannan babban ci gaba ne kuma abin a yaba, ganin cewa ilimi shi ne garkuwar dan Adam, kuma ilimi shi ne silar ci gaban kowace al,umma,
Bayan haka mai girma Ministan Ilimi, a madadin al’ummar Karamar Hukumar Dambam ta Jihar Bauchi, muna neman alfarma da a kawo mana wannan makaranta ta (FCE) a wannan gari namu domin share mana hawayen da ya dade yana ta kwarara a idanuwanmu. Ganin cewa muna nesa sosai kuma mu ne bakin bodar tsakanin Jihar Bauchi, da YOBE, ya sa karatu ya yi mana wahala wanda hakan ya sa dalibai da dama da suka kammala makarantar gaba da firamare suka hakura da karatun suka zauna a gida sakamakon rashin Irin wannan makaranta da kuma karancin kudi, wanda ba kowa ne zai iya daukar dawainiyar barin garin ba, domin ci gaba da karatu,
Da wannan dalilai nake kira tare da fatan Ministan Ilimi (Malam Adamu Adamu) zai dubi al’ummar Karamar Hukumar Dambam da idon basira, wajen amincewa da kawo mana wannan makaranta. A garin Dambam.
Hussaini Abba Dambam, Karamar Hukumar Dambam Jihar Bauchi