Kira ga Musulmi a kan murnar Ranar ’April Fools Day’
Zan fara yin godiya ga Allah (SWT) Mai kowa Mai komai, kuma Mai iko a kan komai. Bayan haka ina godiya ga malamanmu na Sunnah da suka tsaya tsayin daka suke fada mana gaskiya komai dacinta, ina rokon Allah Ya saka musu da alheri. Bayan haka ranar 1 ga watan Afrilun kowace shekara rana ce […]
Zan fara yin godiya ga Allah (SWT) Mai kowa Mai komai, kuma Mai iko a kan komai. Bayan haka ina godiya ga malamanmu na Sunnah da suka tsaya tsayin daka suke fada mana gaskiya komai dacinta, ina rokon Allah Ya saka musu da alheri.
Bayan haka ranar 1 ga watan Afrilun kowace shekara rana ce da YAHUDAWAN duniya suke kira da suna ‘April Fools Day.’ Wato ‘Ranar Shashantarwa.’
Abu na farko da nake so in shaida wa dan uwa Musulmi a kan wannan bakar rana ta ‘April Fools Day,’ shi ne bai kamata a ce Musulmi yana murna da wannan rana ba, kuma duk wanda aka ga yana murna ko taya YAHUDAWA murnar wannan rana, to gaskiya bai san ma’anar wannan ranar ba ce, ko kuma tsabar son zuciya ne ya kai shi ga aikata haka.
Wannan bakar ranar ta samo asali ne a kasar Spain a wani gari da ake kira GARNADA wanda a yau ake kira da suna Granada. A tarihi gari ne da ya tara manyan malamai Ahlus-Sunnah, amma saboda tsabar Yahudanci da kiyayya da Musulunci haka aka rika kama manyan malaman Musulunci nan ana yi musu yankan rago. Saboda a kawar da Musulunci ga doron kasa, ta kai ba su daina kisan Musulmi ba sai da suka kaga sun gama da manya-manyan malaman Musulunci a wancan lokaci. Tarihin garin GARNAƊA da aka yi wa Musulmi wannan kisan gillar a baya daula ce ta Musulunci wadda ta shafe kusan shekara 500 Musulunci yana mulkinta.
Bayan kashe Musulmin ne baya sauran Musulmin da suka rage aka tara su a wuri daya, aka alkawarta musu cewa za a basu wani fili da ke tsallaken ruwa su koma su ci gaba da shari’arsu ta Musulunci kuma babu wanda zai takura musu. Sauran Musulmi a wancan lokacin suka amince da wannan bukatar ta YAHUDAWA, inda a nan ne aka sanya su cikin jirgin ruwa guda sai da aka kai tsakiyar ruwan aka kifar da su suka nutse duk suka mutu.
Nan ne fa YAHUDAWA suka dawo suna murna da farin ciki sun kawar da Musulunci a garin Granada, kuma a daidai wannan ranar.
Tunda haka ta faru duk shekara daidai wannan ranar sai YAHUDAWA sun yi wannan bikin na ‘April Fools Day,’ wato an mai da Musulmi shashasha, kuma wai a haka za a samu wawayen cikinmu suna taya su murnar wannan bakar ranar ta ‘April Fools!’
Allah Ya sauwake Ya kuma raba mu da aikata aikin assha, Ya kara kiyaye Musulunci da Musulmi, Ya kuma ci gaba da dora Musulunci a kan kafirai.
Daga Sulaiman Muhammad Gusau,
Official Labour Room Global Initiative Jihar Zamfara
07067297714.