Kira ga sabon shugaban kasarmu
Kirana zuwa ga sabon shugaban kasar tamu,shi ne ka ga dai yadda azzaluman shugabanni suka mayar da talakan Najeriya ya zama marar galihu.Ina fatan za ka tabbatar mana da zaman lafiya a wannan kasar tamu. Bayan wannan gamu nan matasa da yawanmu ba mu da aikin yi sai dai mu zauna kawai.Ina fatan sabon shugaban […]
Kirana zuwa ga sabon shugaban kasar tamu,shi ne ka ga dai yadda azzaluman shugabanni suka mayar da talakan Najeriya ya zama marar galihu.Ina fatan za ka tabbatar mana da zaman lafiya a wannan kasar tamu.
Bayan wannan gamu nan matasa da yawanmu ba mu da aikin yi sai dai mu zauna kawai.Ina fatan sabon shugaban kasar tamu zai kasance mutum mai sanya ido kan matasa domin ganin muma mun samu aikin yi da za mu dogara da kanmu ba da abin wani ba.
Ina kuma fatan shugaban kasar ta mu zai kasance mutum mai lura da harkar ilimi domin mu matasa muma mu samu mu yi karatu me zurfi domin kai wa matsayin da za mu gaje su a lokacin da ba sa nan don gudun kada azzaluman shugabanni su kara dawowa,domin a yanzu talakawa an hana su karatu.Da can mutum yana yin karatu ne kyauta,amma a yanzu
talakawa koda kudinsa ma karatu ya zame masa wahala ana wulakanta shi.Ina fatan Babanmu, Baba Buhari zai duba mana wannan lamari domin muma mu ji dadi a karkarshin inuwarsa.
Bayan haka ina mai farin cikin taya sabon shugabanmu murnar darewa wannan kujera domin kwato hakkin talakawa,mu mun san kana yi ne ba don abin duniya ba,mun san kana yi ne domin mu,Allah Ubangiji ya ba ka ikon rike amana,tare da tafiyar da mulkinka a kan adalci kamar yadda ka fada.
Usman dan gundumar Jama’are
081-63055770
[email protected]