Kira ga ’yan bindiga masu kashe jama’a

Assalamu alaikum Edita. Hakika wannan aika-aika da ’yan  bindiga ke kashe jama’a tana ci min tuwo a kwarya matuka a matsayina na Musulmi wanda na san darajar ran dan Adam. Haba kai mai kashe rayukan jama’a ka amsa wadannan tambayoyi. * Shin mece ce ribarka don ka kashe mutum dan uwanka? * Shin dadi za […]

Kira ga ’yan bindiga masu kashe jama’a
Kira ga ’yan bindiga masu kashe jama’a

Assalamu alaikum Edita. Hakika wannan aika-aika da ’yan  bindiga ke kashe jama’a tana ci min tuwo a kwarya matuka a matsayina na Musulmi wanda na san darajar ran dan Adam. Haba kai mai kashe rayukan jama’a ka amsa wadannan tambayoyi.

* Shin mece ce ribarka don ka kashe mutum dan uwanka?

* Shin dadi za ka ji ko kuma murna za ka yi don ka kashe ran dan uwanka dan Adam?

* Shin wace riba za ka samu idan wani ya biya ka domin ka je ka  kashe mutum dan uwanka?

*Shin mene ne abin burgewa gare ka don ka sanya dimbin jama’a cikin garari da yawon ‘gudun hijira’ tare da lalata musu dukiyoyinsu da kuma kuntata wa farin cikinsu a rayuwa?

* Shin ko za ka iya tuna mata nawa da dimbin yara nawa ka mayar gwagware da marayu ta sanadiyyar ta’asarka?

* Shin ko kasan cewa hakan cin amanar kasarka kake yi tare da al’ummar kasarka dama kai karan kanka?

* Sannan anya kana tunanin haduwarka da Ubangijinka Mahallinci, inda za ka tsaya a gabanSa tare da mutanen da ka zalunta komai yawansu domin a yi muku hisabi?

*Sannan maimakon gwamnati hankalinta ya tsaya wajen samar wa ’yan kasa kayayyakin jin dadin rayuwa da walwala da kuma abubuwan more rayuwa da ma duba bukatunsu na yau da kullum domin share musu hawaye, sai ga shi ka sa yanzu hankalin gwamnati kwacokan ya karkata zuwa samar da tsaro da nufin tabbatar da zaman lafiya a  yankunan da kake kashe-kashen da jawo rikice-rikice?

*Kana sane da cewa hakan zai sa gwamnati ta samu wata hujja cewa tana kokarin tabbatar da kyautatuwar zaman lafiya ne, duk lokacin da muka nuna gazawarta kan rashin magance talauci da wahalhalun rayuwa da mu al’ummar kasa muke fama da su?

Don haka ina fata wadannan bayanai nawa za su yi tasiri ga masu aikata wannan ta’asa ta kashe-kashe da garkuwa da mutane da satar shanu, su ajiye makamansu koda kuwa sun dauke haka a matsayin sana’a ce domin samun zaman lafiyar kasarmu Najeriya.

Sannan ga gwamnatoci a matakan jihohi da tarayya su fahimci cewa samar wa matasa ayyukan yi da sana’o’in dogoro da kai za su taimaka kwarai wajen shawo kan wannan matsala.

Bissalam Allah Ya sa mu dace amin sum

Daga Hussaini Abba Dambam, Jihar Bauchi.

08020814173.