Kira ga ’yan majalisar jihohin Arewa
Harkar saye da sayarwa da ba da haya ko aron gidaje da shaguna da filaye ta zama sakaka, ta yadda a yanzu ake yin ta a tsakanin mai shi da mai so ko tsakanin dillalai da mai karba ba tare da sani Mai unguwa ko Dagaci ko Limamin gari ba kamar yadda abin yake a […]
Harkar saye da sayarwa da ba da haya ko aron gidaje da shaguna da filaye ta zama sakaka, ta yadda a yanzu ake yin ta a tsakanin mai shi da mai so ko tsakanin dillalai da mai karba ba tare da sani Mai unguwa ko Dagaci ko Limamin gari ba kamar yadda abin yake a da. Hakan yana daya daga cikin manyan abubuwan da suke kara kawo kalubale a fannin tsaro musamman matsalar garkuwa da mutane.
Domin ta haka ne ake samun miyagun mutane suna yin shigar burtu suna shiga cikin unguwanni a kauyuka da birane suna sayen filaye su gina ko su sayi ginannun gidaje su zauna ko kuwa su yi hayar gida ko shago su shiga ciki su yi ta amfani da su suna fakewa da guzuma suna harbin karsana.
Yana da kyau ’yan majalisar jihohin Arewa su yi wata doka da za ta tilasta wa mai saye ko mai sayarwa ko dillali cewa dole sai sun gabatar da kawunansu a gaban sarakunan gargajiya yankin da suke don gabatar da wanda zai saya ko karbar hayar wani gida ko shago ko fili ko wata gona in har ya kasance bako ne a wannan wuri kuma yana son saye ko hayar wata kadara. Ta yadda su sarakunan za su rubuta su ajiye wasu muhimman bayanai game da wanda zai saya ko mai daukar hayar. Wadannan bayanai za su iya kunsar; shin wane ne shi wannan mai saye ko mai karbar hayar? Me zai yi da abin da yake son saye ko hayar? Daga ina ya fito kuma mece ce sana’arsa?
Haka kuma su rubuta su ajiye sunan garinsa na asali, sunayen danginsa da iyalinsa kai har ma da tarihin wata rashin lafiya ko nakasa da shi ko iyalinsa suke da ita. Sannan su samu akalla hotunansa da na iyalinsa in har yana da su.
Wannan doka idan aka aiwatar da ita za ta taimaka wajen takaita wasu laifuffuka da ayyukan ta’addanci da wadansu bakin fuska kan yi ta hanyar samun mafaka cikin al’ummar da ba su da masaniya game da boyayyiyar manufa da niyyarsu. Wanda kuma hakan yana cutar da jama’a da dama ta hanyoyi daban-daban.
Daga Iro Surajo, Abuja, 0816 343 9197