Kira ga ‘yan siyasar Najeriya

Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga daukacin ’yan siyasar Najeriya musamman ma ’yan takarar shugabancin kasa guda biyu wato Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC. Tabbas ya kamata ku sani cewa, nuna wa al’ummar Najeriya muhimmancin dimokuradiyya a lokacin yakin neman zabenku shi ne […]

Kira ga ‘yan siyasar Najeriya
Kira ga ‘yan siyasar Najeriya

Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga daukacin ’yan siyasar Najeriya musamman ma ’yan takarar shugabancin kasa guda biyu wato Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC. Tabbas ya kamata ku sani cewa, nuna wa al’ummar Najeriya muhimmancin dimokuradiyya a lokacin yakin neman zabenku shi ne abin da ya fi muhimmancin ba wai daukar alkawuran da ba za a iya cika su ba. Lallai yana da kyau ku rika koyi da ’yan siyasar kasashen da suka ci gaba wajen bai wa ’yan kasa damar zabar duk wanda ya kwanta musu a rai kuma suke ganin su ne mafita a gare su. Hakika yana da daga cikin amfanin dimokuradiyya a kowace kasa da take amfani da ita ta haramta yin amfani da kudi ko makami a lokacin yakin neman zabe, sannan gwamnati mai ci ba ta isa ta yi amfani da karfin mulkinta ko amfani da jami’an tsaro ba wajen tursasa wa hukumar zabe ba. Hukumar zabe ita ce ke tafiyar da tsare-tsarenta ba wai gwamnati ce za ta tsara mata ba, Ana bai wa dukan ’yan kasa damar yin zabe domin su ake mulka, ita kuwa ma’anar dimokuradiyya ita ce mutane su zabi wanda suke so da kansu ba wai wani ya zaba musu ba. A karshen ina yi wa kasata abar alfaharina wato Najeriya fatar samun shugaba nagari mai adalci. Yarima Ya’u Adamu Bulkachuwa

Daga Jihar Bauchi. 09034444404, 09066738686.