Kira, rarrashi da ban hakuri ga kungiyar Ahlul Sunna Lil’da’awatu

A wannan makon, mun samu tsokaci mai take na sama daga Malama A’isha Usman Liman, [email protected] wadda ta yi rarrashi da ban magana ga ’yan Boko Haram. Ga abin da take cewa:Ya ku ’yan uwa Musulmi kuma ’yan Najeriya, ’yan Jama’atul Ahalul sunna lil’da’awatu wal jihad, ’yan Yusufiya, ’yan Boko Haram; ina yi muku sallama […]

Kira, rarrashi da ban hakuri ga kungiyar Ahlul Sunna Lil’da’awatu

A wannan makon, mun samu tsokaci mai take na sama daga Malama A’isha Usman Liman, [email protected] wadda ta yi rarrashi da ban magana ga ’yan Boko Haram. Ga abin da take cewa:
Ya ku ’yan uwa Musulmi kuma ’yan Najeriya, ’yan Jama’atul Ahalul sunna lil’da’awatu wal jihad, ’yan Yusufiya, ’yan Boko Haram; ina yi muku sallama irin ta addinin Musulinci, Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wabarakatuhu.
Na dora alkalamina ne a kan takarda ba don komai ba sai don ina son in yi amfani da shi, in rarrashe ku, in ba ku hakuri; in kuma ba ku shawara a kan wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki, daga mu har ku, domin mu duka ne muke cikin wannan tashin hankali na rashin zaman lafiya.
Mun yarda da ku Musulmi ne kamar mu, wadanda suka yarda da Allah daya ne kuma Annabi Muhammadu (saw) manzon Allah ne, sai dai akida ce ta bambanta. Wannan kuwa dama akwai shi tun fil’azal a cikin kowane addini.
Ina ganin kowa a kasar nan ya san abin da ya fara kawo rashin jituwa a tsakaninku da hukuma, don haka ba sai mun koma baya an yi tashin-tashina ba. A’a, mu dai abin da muke ganin shi ne, mu yi gaba mu ga ya za a yi mu samu sulhu a tsakaninku da hukuma, wanda zai yi musabbabin dawo da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin garuruwanmu da yankinmu na Arewa da ma kasa baki daya.
Lallai duk wanda aka taba shi ko aka yi masa ba daidai ba sai zuciyarsa ta dugunzuma, ta ji ba ta ji dadin abin da aka yi mata ba, tunda wannan hali ne daga cikin halayen da Allah Ya halicci dan Adam da su. Amma kuma ba ya cancanta ga Musulmi, mumini ya bar wa zuciyarsa ragamar tafiyar da rayuwarsa kacokan, sai yadda ta yi da shi. Wannan ba ya cikin kowace irin akida ta Musulunci, domin yana da illa matuka, saboda fadar Allah (swa):
“Shin ka ga wanda ya riki son zuciya shi ne abin bautawar sa kuma Allah Ya batar da shi a kan wani ilimi kuma ya toshe a kan jinsa da zuciyarsa kuma ya sanya wani rufi a kan ganin sa, to wane ne zai shiryar da shi bayan Allah, shin to ba za kuyi tunani ba?” (Sura 45 Aya 23)
Da za mu yi duba zuwa ga wannan ayar da idon basira, da kuwa mun gane, da ba abin da ya kai mu cikin wannan halin da muke ciki na rashin zaman lafiya da kasha-kashen junanmu da ya ki ci ya ki cinyewa, illa mu ce dokin zuciya, wanda a lokacin muke ganin kamar zai yi sukuwa da mu ya kai mu ga mafita. Sai ga shi ba inda ya kai mu sai kan hanyar da na sani, domin kuwa dukkanmu, (ku da mu da ita kanta hukuma) ba wanda zai ce wannan hali da ake ciki ya ribantu da shi, ko ya yi nasara.
Bari mu dauke shi daki-daki mu gani yadda abun ya zama ba nasara, sai dai hasara da juyayi a gare mu: Ku da aka taba ku, aka yi muku laifi ba bisa hakkinku ba, kuka ki yin hakuri da juriya kamar yadda Allah (swt) Ya umurta, sai kuka hau dokin zuciya, kuka yanke shawarar daukar fansa, ba tare da zurfin tunani ba. Ku ka manta da umurnin manzon Allah (SAW), da ya ce wa wani mutum da ya zo wurinsa, ya ce ya taimake shi da nasiha, sai ya ce masa: “Kada ka yi fushi.” Ya yi ta maimaita masa wannan kalami.
Sai kuka dauka cewa idan kuka yi fito-na-fito da hukuma za ku rama kuma za ku yi nasara. Kun manta da cewa akwai kotuna, kun manta da cewa wannan fitowar za ta iya shafar wasu jama’a, wadanda ba su ji, ba su gani ba. Kun manta wadannan garuruwa, garuruwanku ne, jama’arku, ’yan uwanku, iyayenku, kowa ma naku ne. ’Yan uwana, kuna sane da cewa fitina barci  take, Allah Ya la’anci mai tada ita, kuna sane da cewa in ka san farkon fitina, ba ka san karshenta ba. Kuna sane da cewa Allah (swt) ba ya gafarta wa wanda ya zalunci wani amma kuka runtse idonku, kuka biye wa dokin zuciya, kuka kutsa cikin yaudarar Shedan, kuka manta da hakki ’yan uwanku, kuka kasa koyi da manzon tsira (saw), kuka fusata, kuka maida martani har ma fiye da abin da aka yi maku.
Sanadiyyar wanan fusatar taku, da yawa sun zama marayu, wasu sun zama gwauraye, wasu sun rasa ’ya’yansu masu taimaka masu, wasu sun bar garuruwansu da gidajen su har abada. Da kun yi hakuri, aka dauki abun a kan hanyar sulhu da tattaunawa ko shari’a, da abun bai kai haka ba, tunda dai kowa ya san dokar kasar nan ta ba kowane dan kasa ’yanci  yin addininsa a duk inda yake.
Ya ku ’yan uwa, magana ta gaskiya ku sani wannan halin da muka tsinci kanmu a ciki daga ku har mu, wallahi ya kai mu intaha, koma bayan da ya janyo mana ba su da iyaka kuma ya kamata a ce ya isa haka. Ga uwa uba ita ma hukuma ta runtse nata idon, ta manta da hakkin sauran talakawanta, sai gallazawa take yi ba ruwanta.
Shi ne muke ganin ku ne dai namu, mu kuma naku, iyayenku, ’ya’yanku, kannenku, yayyenku, matanku, surukanku, makwabtanku, jama’arku, garuruwanku, yankinku, kasarku, ku ya fi kamata da cancanta da mu biyo ta hannunku, mu neme ku da ku yi hakuri, ku yi hakuri don girman Allah. Ku aje makamanku, ku saduda. Ba don komai ba, sai don girman Allah da manzonSa, ku dubi halin da danginku da zumuntarku suke ciki. Ku nemi sulhu da hukuma, ku nuna mata kun saduda, kun aje makamai, kun dawo teburin sulhu da ita hakumar. Yin haka ba karamin jihadi ba ne shi ma kuma ladarsa ta fi ladar jihadin da kuke ciki a yanzum, za kuma ku sami yafiyar dangi da ’ya’yan wadanda suka tsinci kansu cikin wannan halin na maraici, gwagwaraci, kewar dangi da ’yan uwan da suka rasu, a sanadiyyar sa su cikin wannan halin da kuka yi.
Don Allah don darajar ma’aikin Allah ’yan uwa ku kara tunani, ku tausaya wa ’yan uwantaka da zumunci da makwabtaka; ku ji tsoron Allah ku ajiye makamanku, ku koma teburin shawara da hukuma, ko ma samu saukin wannan hali na kangi da matsi da cutarwa da tsanani da muke ciki a garuruwanmu da yankinmu, da ma kasa baki daya.